Jiragen Kasan Legas Kano da Ajaokuta Sun Daina Aiki Bayan Harbin wasu Fasinjoji
- Shugaban NRC mai kula da harkokin jirgin kasa a Najeriya yace jirgin Kano-Legas ya daina aiki
- Akwai matsalar tsaro a yankunan Kaduna da Minna, saboda haka aka dakatar da aikin jiragen
- Haka zalika NRC ta tabbatar da cewa jirgin Warri-Itakpe ba zai rika tsayawa a Ajaokuta ba
Abuja - Hukumar NRC mai kula da harkokin jirgin kasa a Najeriya ta dakatar da ayyukan jiragen kasan Legas zuwa Kano da kuma jirgin Ajaokuta.
Tribune ta kawo rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta 2022 cewa NRC ta dauki wannan mataki a madadin gwamnati saboda matsalar rashin tsaro.
Majiyoyi da dama daga hukumar ta NRC sun shaidawa manema labarai cewa an dakatar da aikin jirgin Ajaokuta a dalilin harin da aka kai wa wasu.
A ranar Litinin da ta wuce aka samu ‘yan bindiga sun aukawa fasinjoji a yankin Warri-Itakpe.
Haka zalika rashin tsaron ya yi sanadiyyar daina aikin jiragen kasan Legas zuwa Kano. A dalilin haka aka daina amfani da jiragen Kaduna zuwa Abuja.
Rahoton Punch ya nuna ba za a dawo aiki ba har sai lokacin da aka iya tabbatar za a iya kare lafiyar ma’aikata da fasinjojin da ke bi ta wadannan hanyoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babbar Darektan NRC na kasa, Fidet Okhiria ya tabbatarwa manema labarai cewa jiragen Legas zuwa Kano da na Ajaokuta sun daina aiki a halin yanzu.
Da yake magana game da Warri-Itakpe, Fidet Okhiria ya shaida cewa ba za su dakatar da aiki a hanyar ba, sai dai ba za a rika dakatawa a Ajaokuta ba.
“Dalili kuwa shi ne a jiya (Litinin), yayin da wasu fasinjoji suke barin tashar jirgi a motocinsu, sai aka samu mutane sun buda masu wuta.
Saboda haka sai muka ce ba za mu sake tsayawa a nan ba (tashar Ajaokuta) saboda fasinjoji.”
- Fidet Okhiria
Akwai matsala a hanyar Kaduna/Neja
A bayanin da yayi a ranar Talata, shugaban NRC yace jirgin Warri-Itakpe yana aiki, amma babu maganar a tsaya a Ajaokuta saboda halin da ake ciki a yau.
Baya ga jirgin Legas zuwa Kano, babu wani jirgin kasa da ba ya aiki. Dalilin dakatar da aikin jiragen shi ne matsalar rashin tsaro a yankin Minna da Kaduna.
Tare jirgin Kaduna - Abuja
A watan Maris ku ka samu labari Rotimi Amaechi, a lokacin yana Ministan sufuri, yace ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna-Abuja.
Rotimi Amaechi yace tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, rashin tanadar wadannan kayan aiki ya jawo matsalar.
Asali: Legit.ng