Sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyan albashin watan Yuli

Sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyan albashin watan Yuli

  • Jami'an sojojin Najeriya sun koka akan jinkirin biyan su albashin da suka zargi gwamnatin tarayya ta ki yi
  • Jinkirin biyan albashi mu ya fara zama ruwan dare kuma bamu da ikon yin korafi inji wani jami'in soja da ya nemi a sakaya sunan sa
  • Sojoji sun ce duk da sunyi aiki na musamman bayan harin da yan ta'adda suka kai gidan yarin kuje sai da gwamnatin tarayya ta yi jinkirin biyan albashin su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A daren ranar Talata wasu jami’an sojojin Najeriya da suka hada da na ruwa, kasa da na sama suka yi korafi kan jinkirin da gwamnatin tarayya ta yi na biyan su albashin watan Yuli. Rahoton PUNCH

Wasu Sojoji mazauna Abuja da suka zanta da wakilan jaridar PUNCH wanda suka nemi a sakaya sunansu sun ce, su da takwarorinsu ba su ji dadin yadda gwamnatin shugaba Buhari tare da hafsoshi suka ki biyan su albashin watan Yuli ba.

Kara karanta wannan

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

Sun yi aiki na musamman tun lokacin da aka fasa gidan yarin Kuje da kuma hare-haren baya-bayan nan a babban birnin tarayya Abuja.

soledeir
Sojojin Najeriya sun koka kan rashin biyan albashin watan Yuli FOTO Legit.NG
Asali: Getty Images

Daya daga cikin sojojin ya ce, al’amarin jinkirin biyan albashin su ya fara zama ruwan dare, ko a watan Afrilu gwamnatin tarayya ta jinkirta biyan su albashin su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Su sun kasa fahimtar dalilin da ya sa Shugaba Buhari da hafsoshin soja suka ki biyan su albashi su daidai lokacin da ya kamata.

Wani soja ya ce, sun gaji, kuma abin takaici ne ganin yadda ba za su iya yin korafi Ana zaluntar su amma babu wata hanyar da za su iya kai kukan su.

Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne — Amotekun

A wani labari kuma, Hukumar Tsaro na Yankin kudu maso Yamma mai taken AMOTEKUN ta bayyana cewa babu dan ta’adda guda daya cikin matafiya yan Arewa 170 da ta kama sabanin labarin da ta rawaito a baya. Rahoton Aminiya.Dailytrust

Rundunar ta ce ta gano matafiya za su sauka a garin Ogere na Jihar Ogun, don haka za ta mika su ga jami’an rundunar ’yan Sandan jihar, domin yi musu bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel