Sabon Hari: 'Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 4, Sun Sace Matafiya 14 a Taraba

Sabon Hari: 'Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 4, Sun Sace Matafiya 14 a Taraba

  • Wasu 'yan bindiga sun farmaki wani kauye a jihar Taraba, inda suka hallaka mutane tare da sace wasu da dama
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, harin ya zo ne a ranar Lahadi, kuma an barnata dukiyoyi
  • Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da ke fama da yawaitar harin 'yan bindiga

Gassol, jihar Taraba - Akalla mutane hudu ne suka mutu a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga kimanin 30 a kan babura suka mamaye kasuwar Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol inda suka bude wuta kan wasu ‘yan kasuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ce sun kuma yi awon gaba da mutane shida yayin da ‘yan kasuwa suka bar hajojin su, suka gudu zuwa wani daji da ke kusa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon mummunan hari a Jos

Yadda 'yan bindiga suka tafka barna a jihar Taraba, suka hallaka mutane 4
Sabon Hari: An Kashe ‘Yan Kasuwa 4, An Sace Matafiya 14 A Taraba | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin Umar Tasiu ya shaida wa jaridar cewa harin na ranar Lahadi shi ne na uku da aka kai garin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.

Sai dai, wai rahoton jaridar Punch ya ce mutum uku ne aka hallaka yayin da aka sace mutum shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace wasu mutum 12

A wani harin kuma, wasu ‘yan bindiga sun sace matafiya 14 a hanyar Mutumbiyu zuwa Wukari ranar Lahadi a kauyen Benbel da ke karamar hukumar Gassol da misalin karfe 2 na rana.

An samu labarin cewa ‘yan bindigar da ke barna kan babura sun tare babbar hanyar kauyen Benbel inda suka yi awon gaba da wasu matafiya tare da kwashe dukiyoyinsu.

Rahoto ya ce an ga motoci hudu ciki har da wata babbar mota a wurin da lamarin ya faru.

Wani dan uwan direban babbar motar da aka yi garkuwa da shi ya shaida cewa masu garkuwa da mutanen sun kira waya inda suka bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 30.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Kwache Bajabu Gambo, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma an tsaftace hanyar da ‘yan bindigan suka tare kuma masu ababen hawa sun fara bin hanyar.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon harin da suka kai Filato

A wani labarin, akalla mutane bakwai wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka sake kashewa a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kisan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da wasu mutane 18 suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a yankin karamar hukumar Wase da ke jihar.

Sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Mooulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da kashe-kashen baya-bayan nan na karamar hukumar Jos ta Kudu ga jaridar Punch a Jos a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmaki motar kudi, suka hallaka ma'aikacin banki

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.