Karin bayani: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon harin da suka kai Filato

Karin bayani: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon harin da suka kai Filato

  • An samu tashin hankali yayin da'yan ta'adda suka kai mummunan hari wani yankin jihar Filato a jiya Lahadi
  • An samu wani mummunan hari da ya yi sanadiyyar mutane sama da 18 a yankin jihar, lamarin da ya tada hankali
  • Jihar Filato na daya daga cikin jihohin da ake yawan samun hare-hare tsakanin kabilu a Najeriya

Jos, jihar Filato - Akalla mutane bakwai wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne suka sake kashewa a karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kisan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da wasu mutane 18 suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a yankin karamar hukumar Wase da ke jihar.

Sakataren yada labaran kungiyar Berom Youth Mooulders Association, Rwang Tengwong, ya tabbatar da kashe-kashen baya-bayan nan na karamar hukumar Jos ta Kudu ga jaridar Punch a Jos a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: 'Yan daba sun farmaki coci, sun sace na'urorin buga katin zabe

An kai sabon hari jihar Filato
Yanzu-Yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 7 a wani sabon harin da suka kai Filato | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tengwong ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“An tabbatar da mutuwar mutane bakwai a yankin Danda chugwi bayan wani hari da ‘yan bindiga Fulani suka kai.
“Harin ya faru ne a ranar Lahadi 31/07/2022 da misalin karfe 9:00 na dare.
"Wasu kuma da suka samu munanan raunukan bindiga an kai su asibitin kiristoci na Vom ba su samu kulawar gaggawa."

Sai dai, wani rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, akalla mutane takwas ne suka mutu kana aka kwantar da biyu a asibiti.

Hukumomin tsaro a jihar da suka hada da ‘yan sanda da kuma rundunar soji ta musamman ba su fitar da wata sanarwa ga jama’a dangane da kashe-kashen ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Hakazalika, jaridar Leadership ta ce, jami'an rundunar Operation Save Haven (OPSH) bata yi martani ga wannan barna ba.

Kara karanta wannan

An Gano Gawarwaki 20 A kusa Da Wani Rafi Bayan Harin Yan Bindiga A Zamfara

Harin Bwari: Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 30 da suka kai kan sojoji fadar Buhari

A wani labarin na daban, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da ragargazar wasu 'yan ta'adda 30 da ake zargin sun kai hari kan sojojin fadar shugaban kasa a makon nan.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an kai hari kan sojojin Najeriya a Abuja, inda aka hallaka jami'ai uku tare da jikkata wasu.

Daraktan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ya bayyana aikin da jami'an suka yi a wani taron manema labarai na mako bibbiyu kan ayyukan tsaro a ranar Alhamis a Abuja, rahoton Daily Nigerian.

Asali: Legit.ng

Online view pixel