Bidiyoyi da hotunan raƙashewar 'ya'yan manyan kasar nan a liyafar Yacine da Yaradua, Aisha Buhari ta halarta

Bidiyoyi da hotunan raƙashewar 'ya'yan manyan kasar nan a liyafar Yacine da Yaradua, Aisha Buhari ta halarta

  • An yi gagarumar liyafar cin abincin dare ta kammala shagalin auren Yacine Sheriff da Shehu Yaradua a Abuja inda 'yan uwa da abokan arziki suka dinga tururuwar zuwa
  • Manyan mata a kasar nan da suka hada da Aisha Buhari, Patience Jonathan da kuma Turai Yar'adua, mahaifiyar angon sun samu halarta
  • 'Ya'yan manyan kasar nan da suka hada da Zarah Bala Muhammad, Malah Sheriff, Mahmud Mamman Legas, da sauransu sun haskaka wurin da salon rawansu
  • Amarya da angonta ba a bar su a baya ba, bayan iyaye sun kammala abinda zasu yi, sun kama gabansu, sun sauya kaya inda suka girgije cike da murna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli 2022 ne aka yi kasaitacciya kuma gagarumar liyafar cin abincin dare ta kammala shagalin auren Shehu Yaradua da amaryarsa Yacine Sheriff.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu

Duk da an daura auren tun ranar 23 ga watan Yulin 2022, bayan nan an sake balle sabon shagalin bikin wanda ya dinga samun halartar manyan baki a kasar nan.

Yaraduas
Bidiyoyi da hotunan raƙashewar 'ya'yan manyan kasar nan a liyafar Yacine da Yaradua, Aisha Buhari ta halarta. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Gagarumar liyafar ta samu halartar manyan mutane a kasar nan har da uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba Aisha Buhari kadai cikin matan manyan kasar nan ta samu halartar liyafar ba, uwargidan tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, Patience Jonathan ta samu zuwa wurin.

An bai wa Aisha Muhammadu Buhari damar yin jawabi kafin ma'auratan su yanka kek din auren nasu.

Daga cikin 'ya'yan manyan kasan nan da suka girgije tare da rakashewa a wurin liyafar akwai, Mahmud Mamman Legas, Malah Sheriff, Zarah Bala Muhammad da sauransu.

Hotuna da bidiyo: Alkawari ya cika, an daura auren 'Yaradua da Yacine kan sadaki sisin gwal 24

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun kashe wani babban Basarake a jihar Arewa

A wani labari na daban, 'dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, Shehu Yar'adua ya yi wuff da Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri dake jihar Borno a yau Asabar, 23 ga watan Yulin 2022.

An daura auren a gidan Sheriff wanda yake kusa da barikin Giwa kuma ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilci daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Gwamna Babagana Umara Zulum da takwarorinsa na jihar Kebbi da Jigawa.

Kawun amarya kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya jagoranci wasu jiga-jigai da suka hada da tsohon gwamnan jihar Niger Adamu Mu'azu, tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje, tsohon gwamnan Kastina, Ibrahim Shema, tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aleiro, tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda, tsohon SGF Yayale Ahmed, tsohon gwamnan Zamfara Ahmed Sani Yarima da kuma shugaban NNPC Mele Kyari da sauransu.

Kara karanta wannan

Tinubu, Dangote, Gwamnoni Da Sauran Manyan Masu Fada Aji Da Suka Halarci Auren Diyar Shettima

Asali: Legit.ng

Online view pixel