An Cafke Masu ba ‘Yan ta’adda Sirrin Jami’an Tsaro Wajen Fasa Gidan Yarin Abuja

An Cafke Masu ba ‘Yan ta’adda Sirrin Jami’an Tsaro Wajen Fasa Gidan Yarin Abuja

  • Kwanakin baya ‘Yan ta’adda suka dura gidan gyaran hali da ke Kuje, suka kubutar da mutane barkatai
  • Mutanen da ake tuhuma da laifin tozarta sirrin Jami’an tsaro sun shiga hannun jami’an tsaro a yanzu
  • Ana bincike a kan mutanen da aka cafke domin a gano shugabanninsu da masu ba su taimakon kudi

Abuja - Wasu mutum hudu da ake zargin suna da hannu wajen taimakawa ‘yan ta’adda da sirrin jami’an tsaro sun fada hannun jami’an tsaron Najeriya.

Jaridar PR Nigeria ta rahoto cewa ana zargin wadannan mutane suna da hannu wajen sanar da miyagu game da shige da ficen ‘yan sanda a garin Abuja.

Jami’an leken sirri da na asiri sun tabbatar da cewa sun cafke wadannan mutane dauke da manyan makamai da salular yin waya da bindiga da wasu wukake.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

Rahoton yace an kuma samu tsofaffin wayoyin salula kirar kasar Sin a hannun wadanda aka kama. Wadannan wayoyi da aka samu ba su iya hawa yanar gizo.

Majiyar ta shaida cewa dakarun da suka yi nasarar cafke bakaken waken suna bincike domin gano jagorori da masu taimakawa wadannan mutane da kudi.

Wadanda aka kama suna tsare a hannun jami’an tsaro a Abuja, inda ake yi masu tambayoyi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gidan Yarin Abuja
Bayan an kai hari a kurkukun Kuje Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ana binciken wadanda ke da hannu

A dalilin ta’adin wadannan miyagu ne aka shiga gidan gyaran hali da ke unguwar Kuje a garin Abuja, hakan ya yi sanadiyyar kubutar da mutum fiye da 600.

Vanguard tace ana binciken wadanda aka damke da nufin gano wadanda suke yi wa aiki tsakanin miyagun ‘yan bindiga da kungiyoyin ‘yan ta’addan Boko Haram.

Hukumar DIA masu leken asiri suna ta aiki a boye domin bankado duk wadanda ke da hannu wajen harin da aka kai da sauran ta’adin da ake shirin yi a Abuja.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Gano Gawarwakin Mutum 26 Da Suka Nutse A Ruwa Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi

An kafa wata runduna ta musamman bayan fasa gidan yarin na Kuje da nufin gano masu wannan aiki da wadanda suke taimaka masu da bayanan jami’an tsaro.

Rundunar da aka ba wannan aiki ya hallaka ‘yan ta’adda fiye da 70 zuwa yanzu. Daga cikin wadanda aka aika barzahu akwai wadanda suke tsere daga kurkuku.

An canza GOCs

Kun samu labari sauyin da Laftana Janar Faruk Yahaya yayi a makon jiya ya taba Manjo Janar OC Ajunwa, Manjo Janar AS Chinade da Manjo Janar AA Adesope

An canzawa Manjo Janar S. Mohammed, Manjo Janar, JA Ataguba wuraren aiki yayin da aka fitar da sunayen sababbin GOC da Shugabannin Dakarun sojoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng