Yadda Bidiyon Kyawawan Angwaye Ya rikirkita Mata A Soshiyal Midiya, Wata Tace Angon Take So

Yadda Bidiyon Kyawawan Angwaye Ya rikirkita Mata A Soshiyal Midiya, Wata Tace Angon Take So

  • Yan mata a shafin soshiyal midiya sun mato bayan sun ci karo da bidiyon wasu kyawawan angwaye
  • An dai gano abokanan angon wadanda suka gaji da haduwa suna shashewa tare da yan matan amarya
  • Yayin da wata tace ita angon take so, wasu sun jaddada cewa lallai Allah ya yiwa Hausawa baiwar kyau

Kamar yadda yake bisa al’ada abokai da kawaye kan zage idan aka ce bikin daya daga cikinsu ya taso inda za su kasance cikin duk wasu zirga-zirga da harkoki na bikin.

A kan kuma kulla kyakkyawar alaka tsakanin yan matan amarya da angwaye musamman daga wuraren shagulgulan da ake yi kafin a daura aure irin su kamu, dina da sauransu

Hakan ce ta kasance a bangaren wani ango mai suna Farouk da amaryarsa Fatima, domin abokansu sun basu cikakken goyon baya.

Kara karanta wannan

Al'adun Hausa: Bidiyon Yadda Aka Yi Cinikin Fura Tsakanin Yan Uwan Amarya Da Abokan Ango A Wajen Bikin Fatima Garo

Angwanai
Yadda Bidiyon Kyawawan Angwanai Ya Kirkita Mata A Soshiyal Midiya, Wata Tace Angon Take So Hoto: theweddingstreet_ng
Asali: Instagram

A cikin wani bidiyo da shafin theweddingstreet_ng an gano angwaye da yan matan amare suna shashewa a wajen liyafar dinan auren.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai fa kyawun abokan angon ya kirkita mabiya shafin da dama, har ta kai wasu sun kasa boye maitarsu a fili.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun tofa albarkacin bakunansu kan kyawun mutanen

muneerah_mkay ta yi martani:

“Shin wanda ke sanye da bulun kaya bai da mata?"

safiatoumusa ta ce:

“Ina son angon .”

lyd.ng ta yi martani:

“Gaskiya mu yan arewa muna da kyau dan Allah”

daimlerforeign ta ce:

"Yan arewa na da kyau ..... babu ja a wannan maganar ❤️”

chichi_mb_20 ta ce:

“Mutanen nan na da kyau "

rummyberry ta ce:

“Kyawawan mutane da koina”

treponemas ya ce:

“Dubi yadda gayen nan mai bulun kaya ya lankwasa yarinyar ”

Kara karanta wannan

An Gano Gawarwaki 20 A kusa Da Wani Rafi Bayan Harin Yan Bindiga A Zamfara

daimlerforeign ta ce:

“Tana da miji mai cike da farin ciki ”

Hotuna Da Bidiyo Sun Bayyana Daga ‘Kunshin’ Fatima Shettima

A wani labari na daban, saura kwana daya alkawari ya cika tsakanin Fatima Kashim Shettima da angonta Sadiq Ibrahim Bunu.

Za’a daura auren diyar tsohon gwamnan jihar Borno kuma dan takarar mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima da dan tsohon ministan Abuja, Ibrahim Bunu a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Sai dai kuma, tun a makon jiya ne aka fara shagalin bikin inda aka yi dina wanda ya samu halartan manyan masu fada aji a kasar ciki harda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng