Tsoron ‘Yan Bindiga ya Jawo Dalibai sun Rubuta Jarabbawa 13 a Rana Daya a Abuja

Tsoron ‘Yan Bindiga ya Jawo Dalibai sun Rubuta Jarabbawa 13 a Rana Daya a Abuja

  • Mutane sun shiga halin firgici a wasu yankunan birnin tarayya saboda munanan labaran da aka samu
  • Akwai yiwuwar ‘yan ta’adda su aukawa makarantu, don haka aka bada umarni dalibai su koma gida
  • Kafin a kai ga rufe makarantu, an yi ta laftawa wasu dalibai jarrabawa domin kawo karshen zango

Abuja - A sakamakon halin tsoron da al’umma suka shiga a babban birnin tarayya, hukuma ta bada umarni a rufe duk wasu makarantu da ke aiki a gari.

Wani rahoto da Daily Trust ta fitar, ya bayyana cewa makarantu sun yi maza-maza, sun sa dalibansu sun rubuta jarrabawa kafin a kai ga rufe makarantun.

Ma’aikatar ilmi ta bada wannan sanarwa ne a lokacin da yara suke jarrabawar zango na uku, bayan wannan zango na karshe ne dalibai suke tafiya sabon aji.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Domin ganin sun bi umarnin da ma’aikatar ilmi ta bada, wasu daga cikin makarantu sun tursasawa dalibai, suka rubuta duk ragowar jarrabawarsu a gurguje.

Jarrabawa 13 a rana 1

Wani dalibi mai karatu a makarantar sakandaren Kubwa Model Junior Secondary School da ke garin Abuja ya ba Daily Trust labarin yadda ta kasance da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan yaro yace sun je makaranta ne da nufin rubuta jarrabawa guda ko biyu, amma a karshe sai ga shi a ranar sun buge da rubuta jarrabawar darasi 13.

Dalibai a Abuja
Wata Makaranta a Najeriya Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

Dalibin yake cewa wasu daga cikin yara duk sun gigice da jin labarin yiwuwar harin ‘yan ta’adda.

Haka zalika wata daliba da ke karatu a makarantar kwana a Dutse-Makaranta ta shaidawa jaridar cewa cikin dare aka umarce su da rubuta jarrabawa biyu.

An koma aji cikin dare

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

“Shugabannin makarantan sun kira mu zuwa ajin mu da kimanin karfe 9 na dare a ranar Litinin, suka sa muka rubuta jarrabawa biyu.”

Baya ga haka, a ranar Talata kuma, suka rubuta ragowar jarrabawar da suka rage, yayin da iyayensu suke a harabar makaranta, suna jiran su wuce gida.

Wani malami da aka zanta da shi, ya bayyana cewa saboda gaggawa, ba a kyale dalibai sun amsa duka tambayoyin da aka yi nufin za su amsa ba.

Wuraren da za a iya kai hari

Yanzu haka akwai labarai cewa Yan ta’addan Boko Haram da ‘Yan bindiga sun tare a wasu unguwanni a Babban birnin tarayya na Abuja, za su yi ta'adi.

Miyagun su na kokarin kai hari a wasu makarantu da wuraren da Bayin Allah suke yin ibada. Hakan ta sa jami'an tsaro suka dauki matakan gaggawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng