Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

  • A safiyar yau Talata, 26 ne aka wayi gari da labarin sabon farmakin da yan bindiga suka kai jihar Kaduna
  • Maharan dai sun farmaki unguwar Keke B, Millennium City dake karamar hukumar Chikun ta jihar sannan suka sace mutane da dama
  • Daga cikin wadanda aka sace harda wata uwa da yaranta su uku, kuma tuni aka saki fuskokin wasu daga cikinsu

Kaduna - A daren ranar Litinin, 25 ga watan Yuli ne, wasu 'yan ta'adda suka sake kai mummunan hari unguwar Keke B, Millennium City dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi awon gaba da mazauna yankin.

Yan bindigar sun farmaki yankin ne da misalin karfe 9:00 na dare lokacin da jama’a ke a cikin gidajensu sakamakon ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kanwar Miji Ta Je Har Gida Ta Lakadawa Matar Yayanta Dukan Tsiya, An Gurfanar Da Ita

Maharan sun kuma yi garkuwa da mutane 36 ciki harda wata uwa da ‘ya’yanta su uku.

Wadanda aka sace a Kaduna
Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna Hoto: @harunabakarii
Asali: Twitter

A halin da ake ciki, wani mai amfani da shafin Twitter, Haruna Bakari ya tabbatar da sace yan uwansa guda hudu a harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Bakari, yan uwan nasa da aka sace sun kasance uwa da ‘ya’yanta su uku da kuma dan uwan mijinta.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Innalillahi Wainna Ilayhir Rajiun! Dan Allah ku taya yan uwana da addu’a, an yi garkuwa da su a daren jiya a Keke, Millennium City Kaduna (uwa, yaranta 3 da kanin mijinta).”

Legit Hausa ta zanta da wata mazauniyar unguwar wacce ta nemi a sakaya sunanta, inda ta tabbatar da abun, ta ce an yi garkuwa da wata yar makwabciyarta wacce a ranar ma ta shigo gidanta.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Bayan sake bidiyon azabtar da fasinjojin jirgin Abj-Kad, 'yan bindiga sun sako mutum 3

Ta ce:

“Wallahi kuwa jiya wurin karfe tara suka shigo, ina zaune na ji harbi ya fi karfin takwas a jajjere, ashe suna ta bayanmu ne haka suka dunga buga kofa idan baka bude ba suyi ta harbi har sai ka bude. Wallahi haka suka kwashe al’umma sosai.
“Sun tafi da Yarinyar makociyata. Jiyafa ta shigo gida na.”

DSS Sai Da Ta Gabatar Da rahotannin tsaro 44 Kafin Harin Kuje, In Ji Wase

A wani labarin, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta gabatar da rahotannin tsaro 44 kafin farmakin da yan bindiga suka kai magarkamar Kuje, Daily Trust ta rahoto.

A ranar 25 ga watan Yuli ne yan ta’adda suka farmaki gidan yarin na Kuje sannan suka saki fiye da fursunoni 800 ciki harda dukkanin yan Boko Haram da ke tsare.

Wase ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da gudunmawarsa a kan kudirin dakatar da shirin haramta amfani da babura a fadin kasar da gwamnatin tarayya ke kokarin yi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng