Karfin hali: An kama 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar kungiyar kwadago da ASUU
- Yayin da kungiyar ASUU ta malaman jami'a da NLC ta kwadago suka fito zanga-zanga, an samu dan karamin tashin-tashina
- Rahoton da muka samo ya ce, an kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangan, lamarin da ya tada hankali
- Malaman jami'a sun shafe watanni suna yajin aiki, lamarin da ya kai ga shigar NLC domin jawo hankalin gwamnati
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jami’an tsaro sun damke tawagar 'yan sa kai na bogi yayin zanga-zangar da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da ke yajin aikin a Legas ranar Talata.
'Yan sa kan da aka kama da suka hada da direba da sauran 'yan tawagar sun haifar da wani yanayi na rikici bayan kama wani mai laifi.
Jaridar The Nation ta leka wurin da lamarin ya faru, inda ta ga wasu ‘yan kungiyar sun shiga tsakani a halin da ake ciki amma abin ya haifar da zazzafar cece-kuce.
Sai dai an samu sauki yayin da jami'an tsaron da aka dasa domin kula da zanga-zangar suka shiga lamarin nan take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kama 'yan sa kan na bogi kana aka mika su ga ofishin 'yan sanda. Sai dai ‘yan sandan sun ki yin magana a kai har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Dole za mu shiga lamarin nan: Ganduje ya koka kan ci gaba da yajin aikin ASUU
A wani labarin na daban, gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, a ranar Talata, ya tabbatar wa kungiyar kwadago ta Najeriya cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya a jihar, wadanda suka je gidan gwamnati, inda suka yi zanga-zangar nuna goyon bayansu ga ASUU, rahoton Punch.
Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su mamaye Najeriya domin taya ASUU zanga-zangar nuna fushi
Gwamnan wanda ya koka da rikicin da aka dade ana yi ya ce, kungiyar gwamnoni za ta gana da Gwamnatin Tarayya ta fannin shawarwari domin warware rikicin da nufin ceto tsarin ilimin kasar.
Asali: Legit.ng