Gwamnatin tarayya ta nada Attahiru Jega da sauransu domin su sake duba ga tsarin jami’an Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta nada tsohon sakataren kungiyar makarantun jami’an Najeriya, Farfesa Olkebukola, daga cikin wadanda zasu zaske duba ga tsarin jami’an Najeriya
- Kungiyar ta NUC ta bayyana nazarin auna makarantun jami’a akan mizani da tayi kwanaki a matsayin na jabu
- Ta ce bata auna makarantu jami’a akan mizani ba a kasar tsawon shekaru da dama
Gwamnatin tarayya ta nada wani tsohon shugaban hokumar zabee mai zaman kanta, (INEC), Farfesa Attahiru Jega daga cikin wadanda zasu sake duba ga tsarin makarantun jami’an Najeriya.
Daga ciki wadanda aka nada tare da Jega akwai tsohon sakataren kungiyar makarantun Jami’an Najeriya (NUC) Farfesa Peter Okebukola, jaridar Punch ta ruwaito.
Sakataren kungiyar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed ne ya sanar da nade-naden a wani hira day an jarida a Abuja aranar Litinin, 8 ga watan Janairu, jim kadan bayan ya gurfana a gaban kwamitin majalisar dattawa akan makarantun jami’a da kuma TETFUND domin kare kasafin kudin 2018 da hukumar ta bukata.
Kungiyar ta NUC ta bayyana auna makarantun jami’a aka mizani wanda ta gudanar kwanakin baya a matsayin na jabu.
KU KARANTA KUMA: ‘Yan Siyasan da ke harin kujerar Gwamnan Kaduna a zabe mai zuwa
Ta ce ba’a daura makarantun jamia’an kasar akan mizani ba tsawon shekaru da dama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng