‘Yan bindiga Sun yi Awon-gaba da Mata da Miji Cikin Tsakar Dare a Abuja
- A daren yau aka dauke Sunday Odoma Ojarum da Janet Odoma Ojarume a garin Abuja
- ‘Yan bindiga sun kutsa har gidan na su, suka dauke su a lokacin da al’umma suke ta barci
- Daga baya ‘yan bindigan sun fito da matar da nufin nemo kudin da za a fanshi mai gidanta
Abuja - Masu garkuwa da mutane sun dauke wasu ma’aurata, Mista Sunday Odoma Ojarum da Mai dakinsa, Janet Odoma Ojarume.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da wadannan Bayin Allah a ranar Lahadin nan.
Abin ya faru ne a unguwar Sheda da ke cikin karamar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin Sheda, Japhet Musa ya shaidawa Daily Trust cewa abin ya auku ne a safiyar ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli, 2022.
Japhet Musa yake cewa ‘yan bindigan sun shigo unguwar ta su ne dauke da miyagun makamai.
A cewar mazaunin, masu garkuwa da mutanen sun kafa kansu a wasu sanannun wurare, daga nan suka haura gidan ma’auratan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Musa yace cikin tsakar daren miyagun suka lallaba cikin daren suka dauke Sunday Ojarum da matarsa, Madam Janet Ojarume.
“An shiga dar-dar a kauyen Sheda a ranar Lahadi saboda harbe-harben da masu garkuwan suka rika yi a lokacin.
“Masu garkuwa da mutanen sun fake a wasu muhimman wurare a kauyen, kafin su dauke mutumin da matarsa."
Haka aka yi - Matarsa
A ranar Litinin, matar mutumin ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun shiga gidan na su, tace ta katanga aka hauro masu ana barci.
Kamar yadda ta ke fada, bayan sun dauke su, jagoran ‘yan bindigan ya bada umarni a kyale ta, ta koma gida domin karbo kudin fansa.
Matar ta ce a lokacin da aka shigo gidan, yaransu biyu su na kwance. Har zuwa yanzu dai ‘yan bindigan ba su tuntubi iyalin ba.
Fasinjojin Abuja-Kaduna
Dazu kun ji cewa bidiyon da aka fitar da ya nuna ana lakadawa fasinjojin Abuja-Kaduna duka, ya girgiza mutane a fadin Najeriya.
Wasu ‘yanuwan wadanda ke tsare sun yi niyyar biyar kudin fansa, amma jami’an tsaro suka hana a biya kudin, suka fatattake su.
Asali: Legit.ng