Miyagu sun Bindige Hadimin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Har Lahira
- Jagoran jam’iyyar APC a jihar Delta, Cyril Mudiagbe ya mutu a hannun wasu ‘yan bindiga dadi
- Har gidansa aka shigo, aka bindige Hon. Mudiagbe bayan ‘yan bindigan sun fito daga wani shago
- An rasa gane ‘yan fashi ne ko wasu ‘yan bindiga ne kurum aka aika domin su ga bayan ‘dan siyasar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Delta - Cyril Mudiagbe wanda ya kasance Hadimi a wajen mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar nan, Sanata Ovie Omo-Agege ya mutu.
The Nation ta kawo rahoto cewa Cyril Mudiagbe ya bakunci barazahu ne bayan da wasu ‘yan bindiga suka harbe shi a gidansa a Sapele, a jihar Delta.
Kafin rasuwarsa, Mista Mudiagbe yana cikin jagororin APC a karamar hukumar Sapele, kuma na hannun daman ‘dan takarar gwamna a Delta.
Rahoton ya ce da farko wadannan ‘yan bindiga sun shiga wani katon shago da ke makwabtaka da shi, daga nan sai suka burmo cikin gidan na sa.
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun tari motar gwamnati, sun sheke direba, sun sace fasinjoji sama da 30
Rundunar ‘yan sanda da ‘yan banga sun bazama cikin jeji a karamar hukumar Sapele domin gano wadanda ke da hannu a wajen wannan danyen aikin.
Har zuwa lokacin tattara rahoton nan, ba a samu labarin wadanda suka hallaka Mai ba mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar shawara ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Cyril Makanaki ya kwanta dama
Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto, mutane sun fi sanin marigayin da Cyril Makanaki.
Karin bayanin da muka samu ya nuna an kashe wannan Bawan Allah a unguwarsu da ake kira Decima a Sapele a ranar Asabar, 23 ga watan Yuli 2022.
Da yake abin ya auku ne a cikin dare, sai safiyar Lahadi aka tsinci gawar Makanaki cikin jini.
Wata majiya ta shaidawa jaridar wadannan mutane sun zo gidan Makanaki, suka umarci ya bude masu kofa amma ya ki, sai suka harbe shi ta tagar daki.
Ba fashi da makami ba ne
Ana zargin cewa ‘yan bindigan sun zo ne kurum domin su kashe ‘dan siyasar domin sun bar gidan ba tare da sun dauki komai ba, illa ran shi da suka dauka.
An ruga da shi zuwa wani asibitin kudi, a nan Likitoci suka tabbatar da ya mutu. Kakakin ‘yan sandan Delta, DSP Bright Edafe bai ce komai ba tukuna.
Zaben jihar Delta
A makon da ya wuce, kun ji labari tsohon jigon PDP, Godsday Elder Orubebe yana da farar kafa, shi ne zai jagoranci neman zaben Gwamnan APC a jihar Delta.
A zabe mai zuwa, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ne ‘dan takaran APC, ya zabi Orubebe ya zama masa shugaban kamfe.
Asali: Legit.ng