Gwamnatin Nan Ta Gaza Mana, In Ji Jaruma Maryam Booth Kan Bidiyon Dukan Fasinjojin Kaduna-Abuja

Gwamnatin Nan Ta Gaza Mana, In Ji Jaruma Maryam Booth Kan Bidiyon Dukan Fasinjojin Kaduna-Abuja

  • Jarumar masana'antar Kannywood, Maryam Booth, ta fito ta yi tir da gazawar wannan gwamnati mai ci
  • Maryam Booth ta ce ko tantama babu wannan gwamnati ta Shugaba Buhari ta gazawa al'ummar kasarta
  • Ta fito ta yi magana ne bayan bayyana sabon bidiyo da yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna suka saki, inda suke zane mutanen da ke hannunsu

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Booth ta bi sahun takwarorinta wajen yin tir da sabon bidiyon da yan ta’adda suka saki inda suke jibgan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Maryam Booth a wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram ta bayyana cewa lallai wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gazawa al’ummanta.

Kara karanta wannan

Babu Makawa Sai Mun Tarwatsa Najeriya, In Ji Dan Ta'addan Da Ya Tsere Daga Kuje

Maryam Booth
Gwamnatin nan ta gaza mana, In ji Jaruma Maryam Booth kan bidiyon dukan fasinjojin Kaduna-Abuja Hoto: officialmaryambooth
Asali: Instagram

Jarumar ta bayyana hakan ne a rubuce a kasan bidiyon da miyagun suka saki inda suke ta dukan fasinjojin wadanda suka yi garkuwa da su tun a ranar 28 ga watan Maris.

Ta rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Innalilahi wa inna ilayhir rajiun. Maganar gaskiya ita ce wannan gwamnati ta gaza mana gaba daya.”

Yanzu Haka Gwamnati Zata Zuba Ido Tana Kallo, Ali Nuhu Ya Yi Martani Kan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

A baya mun kawo cewa shahararren jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu ya yi martani a kan sabon bidiyon da yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa na Abuja-Kaduna suka saki.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da sarkin Kannywood ya nuna bacin ransa a kan yadda gwamnati ta zuba ido tana kallon yan ta’adda na cin karensu babu babbaka a kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka Gwamnati Zata Zuba Ido Tana Kallo, Ali Nuhu Ya Yi Martani Kan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Daraktan fina-finan ya tambaya ko haka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta ci gaba da zuba ido ana azabtar da al’ummanta ba tare da cika alkawarin da ta dauka na kare rayuka da dukiyoyin talaka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel