2023: Awanni Bayan Kaddamar Da Abokin Takarar Kwankwaso, Wasu Jami'an NNPP Sun Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jam'iyyar New Nigeria's Peoples Party, NNPP ta gamu da labari mara dadi bayan kaddamar da mataimakin Rabiu Kwankwaso
- Jam'iyyar mai kayan marmari reshen jihar Neja ta rasa jami'anta a kalla guda hudu sakamakon hatsarin mota a hanyar Lambata/Bida
- An tattaro cewa cikin wadanda suka rasu akwai ciyamomin kananan hukumomi biyu na jam'iyyar, direba da shugaban matasa
JIhar Neja - Rahotanni sun bayyana cewa a kalla jami'an jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) guda hudu ne suka mutu a jihar Neja sakamakon hatsarin mota.
Shugaban NNPP na Jihar, Mamman Damisa, ya shaida wa yan jarida a ranar Lahadi, ranar 24 ga watan Yuli, cewa lamarin ya faru a kan hanyar Lambata/Bida a yayin da jiga-jigan jam'iyyar da jam'ianta ke dawowa daga tafiya da suka yi bayan kaddamar da mataimakin Rabiu Musa Kwankwaso.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar Damisa, shugabannin jam'iyyar na kananan hukumomi biyu, shugaban matasan jam'iyyar daya da direba sun mutu a hatsarin, The Punch ta rahoto.
Ya ce:
"Mun rasa biyu daga cikin shugaban jam'iyyar mu na kananan hukumomi, shugaban matasa daya da direba a lokacin da hatsarin ya faru.
"Wasu daga cikin mambobinmu kuma sun jikkata kuma sun hada da shugabannin jam'iyyar mu a kananan hukumomin Gbako, Lapai da Edati."
Ya bayyana sunayen jiga-jigan jam'iyyar kamar haka; Alhaji Mohammed Ibrahim, ciyaman na Agaie, da Baba Usman, ciyaman na Katcha.
Kwankwaso Bai Zagi Kudu Maso Gabas Ba, Ba A Fahimce Shi Bane, Shugaban NNPP
A wani rahoton, Rufai Ahmed Alkali, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, na kasa ya ce kalaman da aka danganta da dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, ba a fahimce su ba, The Cable ta rahoto.
Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua
A ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yana bawa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party, 'muhimmiyar dama' na zama mataimakinsa.
Asali: Legit.ng