Wasu Abubuwa 8 da ya Kamata a Sani Game da Hauhawar Farashin Kaya a Yau
- Farashin kayan masarufi da kusan komai ya tashi a kasuwa, musamman a ‘yan watannin bayan nan
- Baya ga Najeriya, wannan tashin farashiya shafi kasashen Duniya da suka cigaba irin Amurka da Ingila
- Kudin sayen kayan abinci, biyan kudin lantarki, man fetur, tikitin jirgin sama duk sun kara kudi a yau
A wannan rahoto da muka dauko daga Al Jazeera, an yi bayani a kan tashin farashi da tasirin hakan ga al’umma da abin da ya kamata ayi:
1. Menene tashin farashin kaya?
Tashin farashi yana nufin kaya su kara tsada a kasuwa, mutum ya gagara sayen abin da ya saya a baya da irin kudin da ya yi amfani da su a wancan lokacin.
2. Menene yake jawo shi?
Ana samun irin haka ne idan akwai karancin samuwar kaya ko ana yawan bukatarsu a kasuwa. Wani dalili shi ne idan abubuwan sarrafa kayan suka tashi
Rahoton ya ce kudin shigo da kaya yana tasiri wajen tashin farashi, sannan idan kamfanoni suka lura mutane na neman kayansu, ido rufe, za su iya kara kudi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Tashin farashi da wahalar abinci
Idan kaya suka yi tsada a kasuwa, za a samu matsala wajen sayen abinci, wanda hakan zai iya jawo yunwa da rashin samun isasshen abubuwan da ke gina jiki.
4. Wanene abin ya fi shafa?
Cibiyar bincike na Pew Research Center tace kusan kowace kasa ta samu hauhawar farashi daga 2020 zuwa yau. Alkaluma sun nuna kaya sun tashi da 18% a Najeriya.
A Israila, hauhawar farashi a yau ya nunku sau 25. Kasashen da ke biye da kasar sun hada da irinsu Italiya da Girka, inda a nan ma abubuwa sun tabarbare sosai.
A Amurka, jaridar ta ce akwai karancin waken suya da masara, shiyasa masana ke tunanin Najeriya, Aljeriya, Masar, Habasha da sauransu, za su fuskanci matsala.
Tashin hankali: An yi mummunan hadari, motoci 3 sun kama da wuta, mutum 30 sun kone a hanyar Zaria zuwa Kano
5. Me gwamnati za tayi?
Daga cikin yadda gwamnati za ta iya rage tsadar kaya shi ne ta hanyar kara darajar riba a banki. Masana sun ce yin hakan zai sa a rage kashe kudi, sai farashi ya sauka.
6. Yaushe za a kawo karshen lamarin?
Masana tattali su na ganin babu ranar da za a ce kaya za su yi sauki domin abin ya cabe. Idan gwamnati ta dauki matakan da ya dace, ana sa ran ganin sauyi a hankali.
7. Me ya kamata mutane su yi?
Daga cikin shawarar da ake badawa shi ne jama’a su rage facaka, su nemi hanyar rage kashe kudi. Sannan bai kamata a rika cin bashi a yanzu ba, a rika tsumulmula.
8. Yakin Rasha v Ukraine
Farashin alkama ya tashi a kasuwar Duniya a sanadiyyar yakin Ukraine da Rasha. A gefe guda, takin zamani ya yi matukar tsada domin daga Rasha aka fi samunsa.
Masana sun ce tashin alkama da takin zai fi shafan kasashe irinsu Najeriya, Masar, Aljeriya, Ethiopia, Morocco, Zimbabwe, Kenya, Yemen, Pakistan da Turkiyya.
Abinci zai yi wahala
Kwanakin baya aka samu rahoto cewa Gwamnatin Muhammadu Buhari ta hango masifar da al’umma za ta shiga saboda tsadar kayan abinci a fadin Duniya.
Ministan harkar gona, Dr. Mohammad Abubakar ya yi wannan bayani a wajen wani taro. Ministan ya ce kasashe suna fama da rashin ruwa da matsalar noma.
Asali: Legit.ng