Kaddamar Da Shettima: Kungiyar Musulmi Ta MURIC Ta Janyo Ayoyin Bible, Ta Zargi CAN Da Yin Karya
- Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta kare malaman addinin kirista da suka hallarci kaddamar da Kashim Shettima
- Farfesa Ishaq Akintola, shugaban MURIC ya ce CAN ta yi karya na cewa fastocin na bogi ne yana mai cewa an bayyana sunansu
- Akintola ya zargi CAN da yunkurin raba kan yan Najeriya da yin bita da kulli ga kiristoci masu ilimi da suka zabi su hallarci taron kaddamar da Shettima
Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC, ta soki Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, kan maganganun da ta yi game da malaman addinin kirista da suka hallarci kaddamar dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, The Cable ta rahoto.
A ranar Laraba, APC ta kaddamar da Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno a matsayin abokin takarar Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasar jam'iyyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Malaman addinin kirista sanya da kaya irin na Bishop-Bishop, wanda CAN ta bayyana a matsayin na bogi sun hallarci taron.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, Ishaq Akintola, shugaban MURIC ya ambaci wani rahoto da PM News ta wallafa na cewa ba a san malaman addinin kiristan da suka hallarci taron ba a matsayin 'karya'.
"An bayyana sunayen dukkan malaman kiristoci da suka hallarci taron kuma babu na bogi a cikinsu. Ana iya gani cewa CAN ba abin amincewa bane. CAN ta yi watsi da mambobinta wanda ba ma gama-garin kirista bane amma fastoci da bishop masu ilimi. Hakan na nuna wani sashi na shugabannin CAN sun yi wa wasu kiristoci bita da kulli," in ji sanarwar.
"Kasancewa fastoci da bishops da dama sun ki bin umurnin CAN sun hallarci kaddamar da abokin dan takarar APC alama ne da ke nuna rashin ingancin surutun da CAN ke yi kan tikitin musulmi da musulmi," in ji shi.
Hakan na nuna cewa akwai kirista masu ilimi da ke iya banbance dai-dai da ba dai-dai ba kuma sun ki bin umurnin CAN.
MURIC ta janyo wa CAN ayoyin Bible
Akintola ya ambaci ayar Bible, kuma ya zargin CAN da kokarin raba kasa.
"Paul ya ce, 'Kada ku yi wa juna karya' (Colossians 3:9-10), amma shugabannin kiristoci sun yi wa mabiyansu karya. Shugabannin CAN sun yi watsi da gargadin da ke littafin Proverbs, '...Duk wanda ke karya zai tabe' (Proverbs 19:9)."
MURIC ta bukaci CAN ta rufe bakinta ta dena yin karya da nufin raba kan musulmi da kirista.
2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN
Tunda farko, Kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, reshen matasa ta ce babu yadda za ta yi ta bari mambobinta su zabi musulmi da musulmi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023, rahoton Vanguard.
Shugaban kungiyar, yankin arewa ta tsakiya, Owoyemi Alfred Olusola, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a Abuja a ranar Talata, ya ce matasan kirista sun yanke shawarar ba za su goyi bayan hakan ba.
Asali: Legit.ng