Abin da ya sa mu ka ba ‘Dan bindiga sarautar Sarkin Fulani inji Masarautar Zamfara
- Masarautar Yandoto ta kare Mai Martaba Sarkin Yandoto a kan yi wa Adamu Aleiro nadin sarauta
- Kwanakin baya Mai martaba Aliyu Garba Marafa ya nada Adamu Aleiro a matsayin Sarkin Fulani
- Kakakin Masarautar Yandoto ya ce Aleiro ya tuba, kuma ya bada gudumuwa wajen kawo tsaro
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Zamfara - Duk da surutun da mutane suke yi, Masarautar Yandoto ta kare matakin da Mai martaba Aliyu Garba Marafa ya dauka na ba Adamu Aleiro sarauta.
Jaridar Leadership ta rahoto Masarautar Yandoto ta bayyana Adamu Aleiro a matsayin ‘dan bindigan da ya tuba, yake kuma kokarin kawo zaman lafiya.
Masarautar ta ce a halin yanzu sabon Sarkin Fulanin na Yandoto ya taimaka wajen kawo kwanciyar hankali, ya yi sanadiyyar da mutane suka koma noma.
Wannan bayani ya fito ta bakin Mai magana da yawun bakin Masarautar, Alhaji Lawal Magaji.
Hikimar ba Aliero sarauta
Lawal Magaji yake cewa suna daukar Ado Aliero a matsayin wanda ya kawo zaman lafiya a kasar Yandoto, a dalilin ba shi sarauta, yanzu kowa zai koma yin noma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton da aka fitar a ranar Alhamis ya ce Magaji ya wanke Masarautar Yandoto, ya ce nadin sarautar zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a fadin yankin.
“Ya na ta kokarin kawo karshen ta’addanci a kasar nan, kuma mun ga canji. Nada shi Sarkin Fulani zai ba shi iko a kan duka Fulanin da ke masarautar.
Hakan kuma zai ba shi damar sa ido wajen kula da hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa a kasar.
Ina so in yi amfani da wannan dama, in yi kira ga mutane su ga wannan a matsayin hanyar da ta fi dacewa wajen magance matsalar ‘yan bindiga.
Dan Bindigan Da Aka Nada Sarauta a Zamfara, Aleru, Ya Kashe Mutane 100 A Katsina, In Ji Rundunar Yan Sanda
Saboda jagoran ‘yan bindigan nan ya tuba yanzu, yana yakar wadanda suka ki ajiye makamai.”
Wasu mazauna yankin na Zamfara su na ganin nadin sarautar zai taimaka wajen kawo kwanciyar hankali bayan tsawon lokaci suna ta fama da hare-hare.
An dakatar da Sarki
A baya an ji labari gwamnatin Muhamma Bello Matawalle ta dakatar da sabon Sarkin Birnin Yandoto a karamar hukumar Tsafe, Alhaji Aliyu Marafa.
An dakatar da Mai martaban bayan ya yi wa tsohon shugaban 'yan bindiga nadin sarauta. Daga baya aka hana Sarakunan yin nadin sarauta kai-tsaye.
Asali: Legit.ng