Abduljabbar Kabara ya shigar da karar Gwamnatin jihar Kano a gaban babban kotu

Abduljabbar Kabara ya shigar da karar Gwamnatin jihar Kano a gaban babban kotu

  • Abduljabbar Nasiru Kabara ya dauki hayar Lauya, ya kai karar Gwamnati da kotun shari’ar Kano
  • Dalhatu Shehu-Usman ya tsayawa Sheikh Kabara, yana neman a tsaida shari’ar da ake yi da Malamin
  • Lauyan yana zargin ba za ayi wa Shehin adalci ba tun da ya shekara daya a tsare, bai samu babu beli ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Kano, ya tsaida ranar da za a kuma sauraren karar da Lauyan shehin malami, Abduljabbar Kabara ya shigar.

Jaridar Sun ta kasar nan ta ce Sheikh Abduljabbar Kabara ya kai karar gwamnatin jihar Kano a kotu ta hannun wani lauyansa mai suna Dalhatu Shehu-Usman.

Baya ga gwamnatin Kano, malamin da ke gidan yari yana tuhumar babban kotun shari’a na jihar Kano da laifin tauye masa hakkinsa na zama 'dan kasa.

Kara karanta wannan

Lauya ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku Abubakar ya zama Shugabansu

Da aka bijiro da shari’ar a kotun tarayyar a ranar Talata, 19 ga watan Yuli 2022, Dalhatu Shehu-Usman ya shaidawa kotu cewa yana bukatar karin lokaci.

Lauyan ya bukaci lokaci ne domin ya iya duba martanin da bangaren da ake kara suka yi masa.

Ya kamata a daina shari'a da Kabara - Lauya

Shehu-Usman ya nemi Alkali ya bada umarni a dakatar da shari’ar da ake yi a babban kotun shari’a, inda ake tuhumar wanda yake karewa da batanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abduljabbar Kabara
Sheikh Abduljabbar Kabara Hoto; prnigeria.com
Asali: UGC

“Wanda nake karewa ya shafe fiye da shekara daya a gidan yari ba tare da beli ba, kuma ba tare da an dakatar da shari’a ba, ba za ayi masa adalci ba.”

Lauyan Shehi ya gamu da cikas

Lauyan da ya tsayawa malamin musuluncin ya ce kishiyoyinsa su na kokarin fusata shari’ar ne don haka suka gabatar da martaninsu a babban kotun a yau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Umurci A Yi Wa Alkalai Karin Albashi a Najeriya

A dalilin haka, lauyan ya janye bukatarsa a madadin Sheikh Kabara, ya ce babu damar maida martanin da ya dace tun da shari’ar ta dauki wannan salo.

Lauyan Gwamnati bai da ja

Kamar yadda hukumar dillancin labarai na kasa suka kawo rahoto, Lauyan da yake kare bangaren gwamnati, Dahiru Muhammad bai yi jayayya da Usman ba.

Dahiru Muhammad ya roki Alkali ya hana Shehu-Usman gabatar da wani kara da sunan an ci zarafin mutuncin Shehin domin ba wannan ne karon farko ba.

Mai shari’a Abdullahi Liman bai amsa bukatar Kabara ba, ya ki amincewa da rokon dakatar da shari’ar da ake yi, yace za a dawo a ranar 27 ga watan Yuli.

An hana Malamin Lauya a bagas

A watan Yuni ne aka ji labari Abduljabbar Nasiru Kabara ya bukaci a ba shi lauyan da zai kare shi, ba tare da ya biya ko sisi ba, kotu ba ta amince da hakan ba.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Buhari ya fadi abu 1 da zai bar wa ‘Ya ‘yansa gado idan ya bar Duniya

Kwanakin baya kuma an ji cewa Shehin malamin ya zargi lauyoyin da yaudararsa, da kuma damfarar matarsa yayin da yake tsare bisa zargin laifin batanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng