Lauya ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku Abubakar ya zama Shugabansu

Lauya ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku Abubakar ya zama Shugabansu

  • Ebun Adegboruwa SAN ya ba mutane shawarar ka da su sake su zabi Atiku Abubakar a 2023
  • Babban Lauyan ya ce hadamar ‘Da takaran na PDP ba za ta bar shi ya yi aiki idan ya karbi mulki ba
  • Atiku Musulmin Arewa ne irin Buhari, don haka Adegboruwa yake ganin babu adalci idan ya ci zabe

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Wani babban Lauya a kasar nan, Ebun Adegboruwa SAN ya gargadi al’umma da cewa su guji zaben ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar a 2023.

Ebun Adegboruwa SAN ya bayyana adawarsa ne a wani jawabi da ya aikawa Punch. Jaridar ta fitar da wannan rahoto ne a ranar 13 ga watan Yuli 2022.

Lauyan ya zargi Atiku Abubakar da neman mulki ido rufe, yake cewa bai dace a amince kundin tsarin mulki da doka ya fada hannun jam’iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau

Adegboruwa yana zargin jam’iyyar hamayya ta PDP, ta sabawa tsarinta na karba-karba wajen tsaida Atiku a matsayin ‘dan takaranta na shugaban kasa.

Bai dace a ba Atiku tikiti ba - SAN

Wazirin Adamawa ya samu kuri’u 371 a zaben fitar da gwani da aka yi, ya doke Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da kuri’u 237, ratar kuri’u fiye da 100.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Babban lauyan yake cewa hakan ya saba abin da aka san PDP a kai, na yin kama-kama domin ganin mulki ya zagaya tsakanin yankin Kudu da na Arewa.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a Osun Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Buhari da Atiku duk daya ne

Hadarin Atiku ya karbi mulki a ra’ayin Adegboruwa shi ne, irin nacin da yake da shi ba zai bar shi ya yi komai ba, yace haka aka yi da Muhammadu Buhari.

“Tun da yake neman ya gaji Muhammadu Buhari daga shiyyar Arewacin Najeriya, Atiku da magoya bayansa ba su yarda kasar nan ta kowa ba ce.”

Kara karanta wannan

Babban Lauyan Najeriya ya raba gardama game da takarar Musulmi da Musulmi a APC

“Tun da yake neman ya gaji Buhari mabiyin addinin Musulunci, Atiku bai yarda da tsarin mulki cewa kasar nan ta mabiya addinai dabam-dabam ce.”
“Saboda kurum Atiku ya cin ma burinsa na siyasa, PDP ta lashe amanta, ta yi fatali da tsarin mulkinta da adalcin da yake cikin tsarinta na kama-kama”

- Ebun Adegboruwa

Jaridar ta rahoto lauyan yana cewa idan jam’iyyar adawar za ta yi watsi da dokar ta, bai kamata al’umma su amince mata wajen rike tsarin mulkin kasa ba.

Siyasar Kwara

An ji labari Jigon APC, Kayode Ogunlowo zai yi doya da manja a zaben da za ayi 2023, ya bayyana dalilinsa na kin goyon bayan wanda APC ta tsaida takara.

Ogunlowo yana cikin jagororin APC kuma yaran Lai Mohammed, amma sai ga shi a gidan Bukola Saraki, ana tsara yadda PDP za ta lashe zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel