Babu sauran matsalar mai: Shugaba Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na NNPC
- Kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC ya yi sabon tambari a yau Talata, 19 ga watan Yuli
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin mai na NNPC a wani dan taro da aka gudanar a fadar shugaban kasa
- NNPC wanda ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa zai mayar da hankali wajen samar da makamashi na duniya don yau da kullun
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) a ranar Talata, 19 ga watan Yuli.
A wajen taron da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, shugaban kasar ya kuma kaddamar da sabon tambarin NNPC. A yanzu kamfanin ya koma na kasuwanci mai zaman kansa
Da yake jawabi, Buhari ya ce kamfanin man na kasa mafi girma a Afrika zai kuma taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a bangaren tattalin arzikin kasar yayin da yake samar da makamashi ga duniya.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a shafin Twitter, Shugaban kasar ya kuma yi godiya ga Allah a kan yadda ya ke zabar shi domin taka muhimmiyar rawar gani wajen tsara yadda harkar man fetur ke kasancewa a kasar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
“Ina mai godiya ga Allah Madaukakin sarki da ya zabe ni don in taka muhimmiyar rawar gani wajen tsara makomar kamfanin man kasarmu daga mai kyau zuwa mai nagarta.”
Ya kuma bayyana cewa kamfanin zai mayar da hankali wajen zama kamfanin samar da makamashi na duniya wanda zai samar da makamashi na yau , gobe da kuma jibi.
Har ila yau, shugaban kasar ya nuna kwarin gwiwar cewa NNPC Limited zai ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habbaka fannin makamashi a fadin duniya ba tare da dogaro da tallafin gwamnati ba.
Ya ce:
''Daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar 'yan kasuwa, zai zamo wani kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa a fadin duniya, don ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habbaka fannin makamashi a fadin duniya.
''A yanzu doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin."
Buhari ya kuma yi godiya ga shugabanni da mambobin majalisar dokokin tarayya kan yadda suka taka rawar gani wajen ganin an amince da dokar masana’antar Man Fetur (PIA), wadda ta kai ga samar da NNPCL.
Borno: Zulum Ya Biya Naira Miliyan 5 Don Daukan Nauyin Karatun Wani Hazikin Yaro Mai Shekara 13 a Maiduguri
Buhari ya fusata, ya ba ministan ilimi mako biyu ya kawo karshen yajin ASUU
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministan ilimi Mallam Adamu Adamu da ya warware matsalar yajin aikin da kungiyoyin jami’o’i hudu suka dade suna yi tare da kawo masa rahoto nan da makonni biyu.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan da ya karbi wasu bayanai daga ma’aikatu da hukumomin gwamnati da sassan da abin ya shafa wajen sasanta rikicin da ke tsakanin kungiyoyin na jami’o’i da gwamnati.
Idan za a iya tunawa, ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, sannan sauran kungiyoyi su ma suka tsunduma bayan ganin rashin daidaiton sakamako da gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunsu.
Asali: Legit.ng