Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

  • Gwamnan jihar Neja ya bayyana yabonsa ga jaruman sojojin da suka fatattaki 'yan ta'adda a wani yankin jiharsa
  • Rahoto ya ce, an hallaka 'yan ta'adda da dama tare da jikkata wasu a lokacin da suka farmaki sansanin sojoji a Neja
  • Jihar Neja na da yankunan da ke fama da barnar 'yan ta'adda a shekarun nan, an sha dasa sojojin domin shawo kan lamarin

Minna, jihar Neja - Abubakar Bello, gwamnan jihar Neja, ya ce dakarun sojin Najeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan tada kayar baya suka kai a wani sansanin soji da ke yankin Sarkin Pawa a jihar.

A cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN), hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yada labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a ranar Litinin 18 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda a Neja
Yadda sojoji suka ragargaji tsagerun 'yan ta'adda a Neja | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

TheCable rahoto cewa, Bello ya ce maharan sun yi yunkurin kai hari ne a kwaryar garin da kuma kan sansanin sojojin da misalin karfe 2:23 na safiyar ranar Litinin.

Ya ce sojojin da suka amsa kiran gaggawa sun isa garin Sarkin Pawa cikin mintuna 30, kuma an kashe da yawa daga cikin maharan a wani artabu da suka yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

A cewarsa:

"Harin da aka kawo zai yi muni idan da ba don gaggawar mayar da martani daga gwarazan sojojin da ke Sarkin-Pawa da kuma tawagar da suka yi gaggawar amsa kira ba.
“Ba a samu asarar rai a bangaren sojoji ba yayin da aka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
"Amsa kiran gaggawar da sojojin da ke Munya suka yi da kuma martanin da rundunar ta yi game da kiran da suka yi daga Minna abin a yaba ne."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dakile harin ta’addanci kan sansaninsu a jihar Neja

Ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na shawo kan lamarin duk da yanayin da suke ciki na yakar makiya a jihar, Daily Sun ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Gwamnatin jihar Neja ta yaba da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro wajen yaki da rashin tsaro a jihar.”

Ya kuma tabbatar wa da mazauna jihar cewa jihar na hada hannu da gwamnatin tarayya domin ganin an kawar da 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a yankunan manoma da lalata hanyoyin more rayuwa.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jihar Arewa

A wani labarin, jami’an tsaro a jihar Neja sun kashe yan ta’adda sama da guda 200 a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

The Nation ta rahoto cewa an kashe yan ta’addan ne a kananan hukumomin Mariga, Wushishi, Mokwa da Lavun.

Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taro kan lamarin tsaro a jihar ya ce kungiyoyin yan bindiga hudu na ta kai farmaki a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.