Ya yi baki biyu: Yau za a yankewa abokin harkallar Kyari hukunci a shari'ar su Hushpuppi

Ya yi baki biyu: Yau za a yankewa abokin harkallar Kyari hukunci a shari'ar su Hushpuppi

  • A yau 18 ga watan Yuli ne za a yanke wa wani da ake zargin abokin harkallar Abba Kyari ne da ya amsa laifin hannu a damfarar dalar Amurka miliyan 1.1 kan wani balarabe
  • A watan Fabrairu, an gano cewa Yusuf Anifowoshe ya yi baki biyu, inda ya amsa laifinsa bayan da a farko ya musanta hakan yayin da Amurka ke kokarin dauke Abba Kyari
  • A watan Yulin 2021, gwamnatin Amurka ta bude tuhuma kan wasu 'yan Najeriya shida, ciki har da Anifoweshe da Kyari a zargin shirin zamba na $1.1m karkashin jagorancin Hushpuppi

Califonia, Amurka - A ranar Litinin, 18 ga watan Yuli ne wata kotun Amurka da ke gundumar California ta kasar Amurka za ta yanke hukunci ga wani da ya amsa laifinsa na hannu a damfara ta $1.1m da ke zargin Abba Kyari na da hannu a ciki.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

A cewar jaridar Premium Times, wata sabuwar takardar kotu ta nuna yadda Yusuf Anifowoshe ya sauya batunsa na fari, inda ya musanta laifinsa a watan Fabrairu, zuwa sabanin haka, yayin da gwamnatin Amurka ke bin diddigin dauko Kyari daga Najeriya don fuskantar shari’a.

Za a yankewa abokin harkallar Abba Kyari hukunci a Amurka
Damfarar Hushuppi: Wanda aka zargi Abba Kyari dashi ya amsa lafinsa, za a yanke masa hukunci a yau | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ku tuna cewa Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Najeriya da aka dakatar, a yanzu haka na fuskantar tuhuma a Najeriya dangane da alaka da safarar miyagun kwayoyi.

Me yasa Kyari zai fuskanci shari'a a Amurka?

A watan Yulin bara ne dai gwamnatin Amurka ta gabatar da tuhume-tuhume, inda ta zargi mutum shida, ciki har da Anifowoshe da Kyari, da hannu a shirin damfara ta dala miliyan 1.1 karkashin jagorancin Ramon Abass da ake kira da Hushpuppi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotun dai ta Amurka ita ta gurfanar da Hushpuppi a wata kwarya-kwaryar shari'a. Ya amsa laifin damfara ta dalar Amurka miliyan 1.1 kuma yanzu yana jiran a yanke masa hukunci nan da 21 ga watan Satumban bana.

Kara karanta wannan

Buhari Ga Yan Najeriya: Idan Da Kun San Wahalar Da Ake Sha A Wasu Kasashe Da Kun Gode Wa Allah

Manyan tuhume-tuhume 3 da Kyari zai fuskanta a Amurka

A shari’ar da ake kyautata zaton Kyari na da hannu, an tuhumi wasu mutane shida da ake tuhuma da laifin hada baki wajen zamba ta yanar gizo da kuma halasta kudin haram.

Sai dai kuma wadanda ake tuhuma guda uku ne kawai da ke zaune a Amurka suka bayyana a gaban kotun.

Wadannan mutane uku (Anifowose, Rukayat Fashola da Bolatito Agbabiaka) sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma an bayar da belinsu.

Sauran ukun da ke wajen Amurka kuma ‘yan Najeriya sun hada da Kyari, Abdulrahman Juma, da Kelly Vincent. A cewar hukumomin Amurka, har yanzu tana sa ran tabbatar kawo su domin fuskantar shari'a.

Balo-balo: Abba Kyari ya tono batutuwa, ya fadi gaskiyar alakarsa da Hushpuppi

A wani labarin, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya yi zargin cewa matakin da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ya dauka na mika shi kasar Amurka, ba shi da amfani ga shari’a, kana ya yi bayanin alakarsa da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

A daya daga cikin sabbin kararrakin da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja, Kyari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni, ya bukaci mai shari’a Inyang Ekwo da kada ya amince da tasa keyar sa zuwa Amurka domin fuskantar shari’a kan hannu a wata damfara.

Ya yi zargin cewa shirin mika shi Amurka domin gurfanar da shi ba komai bane face nufin hukunta shi, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.