Shugabannin Musulunci da sarakunan Kaduna sun hadu da Kiristoci a coci don yin ibadah tare

Shugabannin Musulunci da sarakunan Kaduna sun hadu da Kiristoci a coci don yin ibadah tare

  • Shugabannin addinin Musulunci da na Kiristanci na kokarin dinke baraka a tsakaninsu gabannin babban zaben 2023
  • Sarakunan Kaduna da wasu manyan Malaman Musulunci sun halarci taron ibadah a coci don amsa gayyatar da aka yi masu na karfafa zaman lafiya
  • Sun yi kira ga mabiya addinan guda biyu da su zamo masu kaunar juna sannan kada su yarda yan siyasa su raba kawunansu saboda son zuciya

Kaduna - Gabannin babban zaben 2023, shugabannin Musulunci da sarakunan gargajiya a jihar Kaduna sun fara yunkurin karfafa hadin kai tsakanin addinai ta hanyar shiga sahun masu ibadah a cocin ECWA da ke hanyar Lemu, Kaduna a ranar Lahadi.

Shugaban kwamitin hulda da jama’a na cocin, Sanata Haruna Azee Zego, ya ce an gayyaci al’ummar Musulmi a yankin ne don su zo su yi ibadah tare cikin aminci a kokarin wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai.

Kara karanta wannan

Da walakin: 'Yan bindiga sama da 100 ne suka halarci taron nada shugabansu sarauta a Zamfara

Zego ya kuma jinjinawa Musulman da aka gayyata kan amsa gayyatar zuwa cocin da suka yi, jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

“Cocin ta gayyace mu ne a kokarinta na karfafa aminci da zaman lafiya a tsakanin addinai, ba tare da la’akari da banbancin addini ba.
“Wasu daga cikin Musulman da suka halarci taron cocin sun kasance yan Nijar da ke zama a ciki da kewayen garin da cocin yake.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin Musulunci da sarakuna
Shugabannin Musulunci da sarakunan Kaduna sun hadu da Kiristoci a coci don wanzar da zaman lafiya Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Sarakunan gargajiyan da suka halarci cocin sune Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubairu; Wakilin Shehu Borno, Mai martaba Bata Madaki Auta, da Sarkin Dutse Alhaji Shuaibu Balarebe Abdullahi da sauransu.

Tattaunawar zaman lafiya

Daga cikin shugabannin Musulunci da suka halarci cocin da kuma yin jawabi kan zaman lafiya tsakanin addinai sune Sheikh Dahiru Abdullahi, Sheikh Dr. Hamisu Ya’u da Sheihk Shehu Ayotola.

Kara karanta wannan

Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha

Duk sun yarda cewa babu wani dalili da zai sa Kiristoci da Musulmi su yi fada maimakon zama masu tsaron juna, rahoton The Sun.

Sun ce:

“Ba za ka zamo Musulmi na kwarai ba idan baka kaunar makwabtanka kiristoci suma kuma haka.
“Ya kamata mu hada hannu sannan mu dawo da baya inda Kiristoci ke alaka da Musulmai tamkar yan uwansu suma kuma haka.
“Musulmai da Kiristoci tagwaye ne. Kiristanci da Musulunci basu canja ba amma Kiristoci da Musulmai sun canja kuma mutane sun yi nasarar raba kan addinan biyu saboda son zuciyarsu.
“Ya zama dole mu dawo da baya inda Kiristoci da Musulmai ke kallon juna a matsayin yan uwa.”

Sheikh Dr. Ya’u, babban sakataren Masallacin Sultan Bello ya bayyana cewa:

“Shaidan shine babban matsalarmu kuma ya zama dole mu hadu don yakar shaidan.
“Ya kamata a girmama dan Adam sama da addini kuma mu yarda da juna kamar yadda muke.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

“Dole mu so junanmu kuma kada mu bari yan siyasa su yi wasa da hankalinmu saboda tsarin siyasa a yanzu zai iya haifar da tarin matsaloli ga Najeriya.
“Kada mu bari yan siyasa su gwara kanmu. Ya zama dole mu hadu a matsayin tsintsiya madaurinki daya sannan mu bari yan siyasa su yi abubuwansu.”

Allah ya la'anci Najeriya shiyasa komai ya lalace, Tsohon wazirin Katsina ya kafa hujja da Alkur'ani

A wani labari na daban, tsohon Wazirin Katsina, Farfesa Sani Abubakar Lugga ya bayyana cewa abubuwa na ci gaba da tabarbarewa a Najeriya duk da addu’o’in da al’ummar kasar ke yi a kullun saboda kasar na karkashin la’antar Ubangiji.

Farfesa Lugga ya ce hakan ya faru ne sakamakon rashin shugabanci nagari, yana mai jan ayoyi daga Al'kur'ani mai giema da littafi mai tsarki.

Wazirin Katsina na biyar ya yi wannan martanin ne a gidansa yayin da yake zantawa da wasu manema labarai a daren ranar Juma’a, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mun daina bacci har sai Tinubu da Shettima sun gaje Buhari, Matasan APC a arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng