Yadda Boko Haram suka nemi sace ‘Ya ‘yan Abokin takaran Tinubu, Kashim Shettima

Yadda Boko Haram suka nemi sace ‘Ya ‘yan Abokin takaran Tinubu, Kashim Shettima

  • Kabiru Umar Sokoto ya taba shirya yadda zai yi awon gaba da ‘Ya ‘yan Sanata Kashim Shettima
  • A sa’ilin da wannan abin ya faru, Kashim Shettima ya zama Gwamna kenan, bai dade kan karaga ba
  • ‘Dan ta’addan ya shiga har gidan Gwamna, kafin ya kai ga taba yaran, jami’an tsaro suka cafke shi

Abuja - Kabiru Umar Sokoto, wani ‘dan ta’addan Boko Haram da aka samu da laifi, yana kitsa yadda zai sace ‘Ya ‘yan Kashim Shettima, sai dubunsa ta cika.

Wani rahoto na musamman da The Cable ta fitar, ya nuna an kama Kabiru Sokoto a gidan gwamnan Borno a Abuja a 2012, amma ya tsere daga hannun hukuma.

Daga baya an sake cafke ‘dan ta’addan a garin Taraba, aka kai shi kotu. Bayanan sirri sun nuna Sokoto ya yi kokarin ya yi garkuwa da ‘ya ‘yan gwamnan Borno.

Kara karanta wannan

Abin da Shehu Sani ya sani game da alakar Abokin takarar Tinubu da Boko Haram

A lokacin, Kashim Shettima ne gwamna a jihar Borno, kuma ya dauke ‘ya ‘yansa daga Maiduguri zuwa birnin Abuja saboda barazanar tsaro da ake fuskanta.

Za a nemi kudin fansa

Jami’an tsaro sun rubutawa Gwamnan takarda cewa ‘Yan Boko Haram su na kitsa yadda za su dauke yaran da ya haifa, domin su bukaci a biya su kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Cable ta ce duka-duka, Shettima bai kai shekara daya da hawa mulki a lokacin ba. A yau shi ne ‘dan takarar mataimakin shugaban kasan APC na 2023.

Kashim Shettima
Sanata Kashim Shettima da Minista Abubakar Aliyu Hoto: @sadiqatfifty
Asali: Twitter

Gargadin da aka yi wa gwamnan ya sa ya tattara yaransa; mata biyu da namiji daya zuwa makarantun wasu kasashen waje da ke Wuse II da Gwarimpa a Abuja.

Lokacin ba a san Sokoto ba

A takardar da aka aikawa Mai girma gwamnan, an sanar da shi cewa wani mai suna Sokoto, ya yi basaja kamar Babarbare, domin ya shiga inda ‘ya ‘yansa su ke.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan ta’adda suka kula da mu inji Fasinjan Jirgin Abuja-Kaduna da ya kubuta

Haka kuwa aka yi, a ranar 14 ga watan Junairu 2021, Kabiru Sokoto ya kutsa gidan gwamnan na Abuja, a lokacin babu jami’an tsaro sosai da suke gadin gidan.

Ahmed Sanda yana rike da kujerar Sakataren din-din-din na gidajen gwamna da suke Asokoro da Maiduguri, ya ba Kabiru Sokoto wurin kwana na dare daya.

‘Dan ta’addan ya yi karyar cewa hanya ta rutsa da shi ne, don haka yake neman masauki. Ashe shi kuwa yana shirin yadda zai dauke ‘ya ‘yan gwamna ne.

Bayan dare daya a wannan katafaren gida, sai jami’an tsaro suka yi ram da Sokoto. Niyyarsa sai an biya Naira Biliyan 1 zai saki yaran, da ya iya cin ma manufa.

An sa Osinbajo zai bar APC?

Mai taimakawa Yemi Osinbajo wajen hulda da jama’a, Laolu Akande ya yi bayani a kan takardar da ke yawo na cewa Mataimakin Shugaban kasa zai bar APC.

Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, bai rubuta wani abu sam mai kama da wannan ba, haka Laolu Akande ya fadawa manena labarai

Kara karanta wannan

Yanzun nan: An yi ram da daya daga cikin wadanda suka tsere daga kurkukun Kuje

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng