An kuma: Daya daga mahajjatan Najeriya ta rasu bayan dawowa da tsayuwar Arfah

An kuma: Daya daga mahajjatan Najeriya ta rasu bayan dawowa da tsayuwar Arfah

  • Allah ya yiwa daya daga cikin mahajjatan Najeriya rasuwa jim kadan bayan kammala tsayuwar Arfah
  • An ruwaito cewa, Hajiya Hasiya Aminu ce ta biyu a cikin 'yan Najeriya da suka riga mu gidan gaskiya a Hajjin bana
  • Wasu da ke kusa da ita, sun bayyana yadda aka yi matar ta rasu, da kuma matakin da ake dauka1

Arfah, Saudiyya - Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wata daga cikin mahajjatan Najeriya mai suna Hasiya Aminu daga jihar Kaduna ta rasu.

An ce hajiyar ta rasu ne bayan ta dawo daga filin tsayuwar Arafat da yammacin jiya Juma'ah 8 ga watan Yuli.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ma’aikata kuma na kungiyar likitocin Najeriya a tawagar mahajjata, na hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) Dakta Usman Galadima ya ce ba a tantance dalilin mutuwar ta ba.

Matar da ta rasu a aikin Hajji
An kuma: Daya daga mahajjatan Najeriya ya rasu bauan dawowa da tsayuwar Arfah | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: AFP

Alhazai da ke kusa da ita a tantinsu sun ce nan da nan da ta dawo, ta kwanta barci daga nan ta gangara barzahu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dakta Galadima ya ce tuni aka sanar da iyalanta kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, rahoton Tribune Online.

Hasiya Aminu ita ce mahajjaciya na biyu da ta rasu a aikin Hajjin bana 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ita ma ta rasu a makon jiya bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarta a Makkah.

Tsayuwar Arafah na tsawon yini ya zama wajibi ga kowane mahajjaci domin cikar aikinsa.

Alhazan Najeriya na daga cikin sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin shekarar 2022 a Arafat.

Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arfah

A wani labarin, sama da alhazai miliyan daya ne suka yi dafifi a Dutsen Arafah domin gudanar da aikin Hajjin 2022, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Tsayuwar ta tsawon yini a Arafat na daya daga cikin manyan abubuwan da ake gudanarwa a aikin Hajji bayan fara a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa tsayuwar Arafah muhimmin bangare ne na aikin Hajji domin wuri ne da Allah ke karban dukkan addu'o'in da mahajjata ke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel