Tsayuwar Arafah: Ku saka su Buhari da kasa a addu'a, Sarkin musulmi ga 'yan Najeriya

Tsayuwar Arafah: Ku saka su Buhari da kasa a addu'a, Sarkin musulmi ga 'yan Najeriya

  • Sarkin musulmi ya yi kira ga musulmai a Najeriya da su saka shugabanni a addu'a a ranar Arafah
  • Ya kuma roke su da su yiwa kasa aduu'ar zaman lafiya da tsira yayin da musulmai ke ayyukan hajji
  • A bangare guda, ya kuma yi kira ga kowa yayi kankan da kai ya mai da komai ga Allah domin samun mafita

Najeirya - Sarkin Musulmi kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmi na gida da na Saudiyya da su yi wa kasa da shugabanninta addu’a.

A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar, ya bukaci al’ummar Musulmin Najeriya da su azumci ranar Arafa kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya umarce su da rokon Allah ba tare da yankewa ba.

Kara karanta wannan

Da walakin: Shugaban Majalisa ya ce akwai hadin-baki wajen fasa gidan yarin Kuje

Sarkin musulmi ya nemi a yiwa shugabanni addu'a a ranar Arafah
Tsayuwar Arafah: Ku saka su Buhari da kasa a addu'a, Sarkin musulmi ga 'yan Najeriya | Hoto: voahausa.com
Asali: UGC

Haka kuma ya roki alhazan Najeriya da su yi wa Najeriya da shugabanninta addu’a musamman a lokacin da suke tsaye a Arafat, Daily Trust ta ruwaito.

Wani bangare na sanarwar yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mai martaba ya yi kira ga al’ummar Musulmin Najeriya don Allah su roki Allah da ya kawo mana karshen kalubalen da ke addabar kasar nan."

Hakazalika, ya kuma roki musulmi da su zama masu kankan da kai wajen mika riko ga Allah, rahoton Independent.

Ya kara da cewa:

“Ya hure mu duka da mu yi ta addu’o’i na musamman kan duk wani bala’i da annoba (na rashin tsaro, talauci, tsadar rayuwa da rashawa) da ke faruwa a Najeriya.
“Hakazalika, yayin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa, muna kuma bukatar mu nemi taimakon Allah da ya datar damu domin samun kwanciyar hankali, tsaro, zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukuncin azumi a Juma'a idan ya yi kicibis da lokacin Ranar Arafah a Musulunci

“Babu shakka, a matsayinmu na masu imani dole ne mu mika kanmu ga Allah, musamman ma cewa duk kokarin da ake yi na maido da zaman lafiya ya ki kai wa ga gaci; duk da haka muna sake nanata cewa bukatar yin addu'a mai zurfi don samun sauye-sauyen siyasa cikin lumana, da kuma kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki daban-daban na da matukar muhimmanci."

Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

A wani labarin, farashin raguna ya karu sosai a duk fadin kasar nan gabanin bikin Eid-el-Kabir (babbar Sallah) na wannan shekara 2023.

A kasuwar Oluwaga da ke unguwar Ipaja a jihar Legas, ana sayar da kananan raguna daga N80,000 zuwa N100,000, matsakaita kuwa tsakanin N120,000 zuwa N180,000, ana sayar da manyan raguna daga N250,000 zuwa N350,000.

Wani dillalin rago a kasuwar, wanda ya bayyana sunansa da Muhammad, ya shaidawa TheCable cewa farashin raguna ya tashi matuka saboda farashin sauran kayayyakin ma ya tashi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu na babbar Sallah 2022

Asali: Legit.ng

Online view pixel