Kuje: Yadda ‘Yan ta’adda suka raba kudi, suka yi wa’azi kafin sakin ‘Yan gidan yari

Kuje: Yadda ‘Yan ta’adda suka raba kudi, suka yi wa’azi kafin sakin ‘Yan gidan yari

  • Kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP) ta dauki nauyin fasa gidan yarin Kuje
  • Rahotanni sun ce sai da ‘yan ta’addan suka tsaya suka yi wa’azi kafin su kubutar da mutanensu
  • Baya ga wa’azi, an rabawa wadanda aka kubutar kudi domin su hau mota, su sulale daga Abuja

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - ‘Yan ta’addan da suka kai hari a gidan gyaran hali da ke Kuje a garin Abuja, sun rabawa wadanda ke tsare kudi kafin su sake su domin su sulale.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Juma’a 8 ga watan Yuli 2022 da ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun ba mutane kudi da nufin samun na hawa mota.

Fiye da mutane 800 suka tsere a daren Laraba daga gidan mazan, amma ana cewa an kamo 400 a cikinsu, wasunsu kuma su na ta dawowa a kan gashin kansu.

Kara karanta wannan

Majiyoyi: Dalilin da yasa maharan jirgin kasan Kaduna suka farmaki magarkamar Kuje

Bayan ‘yan ta’addan Islamic State in West Africa Province (ISWAP) sun iya kutsawa gidan yarin, sun fadawa wadanda ke da niyyar fita cewa za su iya sulalewa.

Wata majiya ta shaida cewa ‘yan ta’addan na kungiyar ISWAP ba su tursasawa kowa tafiya ba, amma sun fadawa masu niyyar sulalewa su hadu da su a waje.

Da aka hadu a wajen gidan yarin na birnin tarayya Abuja, akwai motoci da ‘yan ta’addan suka tanada domin tsofaffin mayakan Boko Haram da ke zaman kaso.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

gidan yari
Bayan kai hari a gidan yarin Kuje
Asali: UGC

Bayan sun shiga motocin, sai suka raba masu kudi da za su yi zirga-zirga, har su batar da sahu.

Jaridar ta ce ‘yan ta’addan sun yi wa wadanda ba ‘yan kungiyarsu ba ne barazanar cewa ka da su shiga motocinsu, an nuna za a kashe duk wanda ya shiga motocin.

Kara karanta wannan

Jirgin Sojoji ya samu akasi, an yi wa Bayin Allah wuta ana zaune kalau a Katsina

“’Yan ta’addan sun fitar da mutane daga gidan kason zuwa wani fili a waje, suka gabatar da wa’azin Kur’ani na kusan tsawon minti 15.”
“Bayan nan sai suka shiga raba kudin mota ga ‘yan kungiyarsu da suka shirya domin su kubutar. Ta tabbata sun yi tanadi da kyau.”

- Majiya

Wani rahoto daga FIJ ya tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun yi wa’azi ne a harshen Fulanci da Hausa, sannan aka yi magana da Ebira ga wadanda suke fahimta.

Da hannun 'yan cikin gida - Majalisa

Ku na da labari Ahmad Lawan ya ziyarci Kuje bayan abin da ya faru, ya ce akwai hadin-bakin wasu da ke aiki a kurkukun ko wadanda suka san kan gidan

Sanata Lawan ya ce bai kamata mutum 300 su aukawa kurkuku, ba tare da jami’an tsaro sun yi hobbasa ba, sai idan akwai abin da aka shirya da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng