Zargin batanci: An yi kaca-kaca tsakanin alkali da lauyan Abduljabbar Kabara a Kotu

Zargin batanci: An yi kaca-kaca tsakanin alkali da lauyan Abduljabbar Kabara a Kotu

  • An yi dirama a zaman kotu tsakanin lauyan Abduljabbar Kabara da alkali inda lauyan ya kwashe komatsansa ya bar kotun saboda tsabar fusata da yayi
  • Tun farko ya soki tambayar da lauyan gwamnati ke wa Kabara sannan ya bukaci shigar da cewa basu da tuhuma a gaban kotun
  • Sai dai alkali yace bashi da karfin ikon cewa basu da tuhuma a gaban kotu tunda Kabara ya fara kare kansa, amma yana da ikon kalubbalantar zargin da ake masa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - An yi karamar dirama a yayin zaman kotu kan shari'ar fitaccen lamain Kano, Sheikh Abduljabbar Kabara, a ranar Alhamis yayin da lauyan malamin, Dalhatu Shehu Usman ya fice ya bar alkali a zauren kotun, Daily Nigerian ta ruwaito..

Gwamnatin jihar Kano tana zargin Kabara da aikata laifuka hudu da suka hada da zargin kalaman batanci kan Annabi Muhammad a ranakun 10 ga watan Augusta da 20 da gwatan Disamban 2019.

Kara karanta wannan

Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin

Abduljabbar Kabara
Zargin batanci: An yi kaca-kaca tsakanin alkali da lauyan Abduljabbar Kabara a Kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A ranar 23 ga watan Yuni ne lauyan wanda aka yi kara ya roki kotu da ta saki wanda yake kare wa saboda dukkan zargin da ake masa ba na shari'a bane.

A zaman yau, Shehu-Usman ya roki kotu da ta bai wa wanda yake kare wa damar shigar da cewa bashi da wata tuhumar amsawa a gaban kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan wanda ake kara ya caccaki tambayoyin da wadanda ke kara suke wa wanda yake karewa kuma ya yi barazanar ficewa daga kotun.

"Akan mene masu kara zasu dinga tambayar wanda ake kara lokacin da mahaifinsa ya rasu? Baya kunshe a cikin zargin," yace.

Tun farko, alkalin ya amincewa lauyan masu kara da ya cigaba da tambayoyinsa kuma lauyan wanda ake karewa ya tattara komatsansa tare da ficewa daga kotun.

Ya kara da bukatar a bashi kwafin takardun shari'ar inda ya kara da cewa zai kalubalanci hukuncin a kotu ta gaba.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Kotu ta ba Sanata Okorocha izinin tafiya jinya kasar waje

Lauyan masu kara, Yakub Abdullahi, ya caccaki bukatar lauyan me kara wanda yake cewa basu da wata tuhumar amsawa a gaban kotu, inda ya kara da cewa malamin ya fara kare kansa a kotun.

Abdullahi ya ce tsohon lauyan wanda ake kara, Ambali Muhammad, SAN, ya sanar da kotu cewa bashi da burin shigar da cewa basu da tuhumar amsawa a gaban kotun a madadin wanda yake karewa.

A yayin tambayoyi, Abdullahi ya tambaya Kabara lokacin da mahaifinsa ya rasu kuma shekarunsa nawa a lokacin?

"Bayan rasuwar mahaifinka, a ina ka cigaba da karatu?" Ya tambaye shi.

Wanda ake kara ya sanar da kotun cewa Sheikh Dr Nasir Kabara ya rasu a 1996.

"A lokacin ina shekaru 25 ko 26 da haihuwa kuma bayan rasuwarsa ban sake halartar wata makaranta a Najeriya ba"

Alkali mai shari'a, Ibrahim Sarki Yola, yace lauyan wanda ake kara yana da damar kalubalantar zargin da ake yi wa wanda yake karewa a kowanne mataki na shari'ar.

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Sai dai kuma ya tabbatar da cewa, lauyan bashi da karfin ikon cewa basu da wata tuhuma a gaban kotu bayan wanda yake karewa ya fara kare kansa.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2022.

Yadda rigima ta kaure tsakanin Abduljabbar Kabara da Lauyoyinsa har ta kai Alkali ya daga shari’a

A wani labari na daban, jama’a sun ga abin mamaki da aka koma babban kotun shari’a da ke Kofar Kudu, garin Kano a shari’ar da ake yi da Abduljabbar Nasiru Kabara.

Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa shehin malamin da ake zargi da batanci da cin mutuncin Annabi (SAW) ya zargi lauyoyinsa da yin ba daidai ba.

Kamar yadda kuka samu labari, da aka koma kotu a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, 2021, Haruna Magashi ya bukaci damar su daina kare malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng