Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin

Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin

  • Sarkin wani karamin kauye a Mexico mai suna San Pedro Humelula ya auri Kada da ta sanya kayatacciyar rigar aure a shagalin bikin
  • Victo Hugo Sosa ya kara da kulla alakar auren ta hanyar sumbatarta a matsayin wani bangare na daddaden al'ada don kawo yalwa ga kauyen
  • An yi imani Kada na wakiltar uwa abar bauta, wanda aurenta da basaraken gargajiyan na nuna hadaka tsakanin mutanen yankin da Ubangijinsu

Ko kana tunanin ka gama ji da ganin abun al'ajabi? To ga labarin wani Sarki a Mexico da ya auri Kada wanda zai daure maka kai.

Rahotanni sun bayyana yadda Sarkin, Victor Hugo Sosa na kauyen Pedro Humelula ya auri kada da ke sanye da rigar aure tare da kulla alakar aure ta hanyar sumbatarta cike da soyayya.

An gano yadda shagalin bikin ya kasance wani bangare na al'ada don kawo yalwa ga kauyen kudu maso yammacin Mexico.

Basrake ya auri kada
Bidiyon auren basarake da kada, ya sumbaceta cike da kauna a kayataccen bikin. Hoto daga Patson Victor Sikazwe Page - MIE/Facebook, Voice of America/Facebook
Asali: Facebook

Auren al'adar da aka dauki tsawon zamunna ana yi tun kaka da kakannni a kasar Oaxaca Chontal da Huave a yankunan gargajiya, kamar irin wata addu'a don neman yalwar arziki daga zamani, kamar yadda Voice of America ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Daily Mail ta ruwaito yadda aka yi imani Kadai mai shekaru bakwai, wacce ake kira da 'yar karamar gimbiya, ke wakiltar Uwa duniya kuma aurenta ga basaraken na nuna hadaka tsakanin mutanen yankin da abun bautarsu.

An daure bakin Kadar, wanda karara hakan ya nuna don kaurace wa hotunan da ba a so ne.

Yayin jawabi game da bikin al'adar, basarake Sosa ya ce: "Muna rokon zamani isashshen ruwan sama, isashshen abinci, kuma muna bukatar samun kifi a kogi."

Hotuna da bidiyon gagarumin bikin da wadanda suka halarta cikin farinciki yayin da suka yi rawa ga wakar gargajiya da mutane da dama na kambama basaraken yayin da yake sumbatar sabuwar amaryarsa.

Hotuna: Matashin da ya tsinta jariri a titi shekaru 4 da suka wuce, ya saka shi makaranta

A wani labari na daban, wani matashi mai karancin shekaru mai amfani da shafin @kala_kakapentoa ya nuna halin tausayi da jin kai wanda ya dace mutane su yi koyi da shi.

A wani bidiyo da ya wallafa a shafin, mutumin ya hada hotunan jinjirin a ya tsinta a jefen titi bayan shekaru hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel