Yadda rigima ta kaure tsakanin Abduljabbar Kabara da Lauyoyinsa har ta kai Alkali ya daga shari’a
- Sheikh Abduljabbar Kabara ya yi kaca-kaca da lauyoyinsa da aka koma kotu
- Shehin malamin ya zargi lauyoyin da yaudararsa, da kuma damfarar matarsa
- Lauyoyin da suka tsaya wa malamin sunce duk abubuwan da ya fada karya ne
Kano - Jama’a sun ga abin mamaki da aka koma babban kotun shari’a da ke Kofar Kudu, garin Kano a shari’ar da ake yi da Abduljabbar Nasiru Kabara.
Jaridar Daily Trust ta samu labari cewa shehin malamin da ake zargi da batanci da cin mutuncin Annabi (SAW) ya zargi lauyoyinsa da yin ba daidai ba.
Kamar yadda kuka samu labari, da aka koma kotu a ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, 2021, Haruna Magashi ya bukaci damar su daina kare malamin.
Alkali mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da rokon Haruna Magashi a madadin sauran lauyoyin, ya nemi malamin ya dauko hayar wasu lauyoyin.
Me Abduljabbar Nasiru Kabara ya fada game da lauyoyin?
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya jefi lauyoyin na sa da laifuffuka da-dama, yace lauyoyin sun umarce shi ya nuna yana da tabin hankali a gaban likita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton yace malamin ya shaida wa kotu cewa tsofaffin lauyoyin na sa sun umarce shi ya yi gum a kan sababbin laiffukan da ake tuhumar shi da su a kuliya.
Sheikh Abduljabbar Kabara yake cewa wadannan lauyoyi sun kuma hada-kai da wani babban jami’in gwamnati, suka karbi N250, 000 a hannun matarsa.
Har ila yau, Sheikh Kabara ya fada wa Alkali cewa lauyoyin sun karbi N300, 000 da sunan za su wanke shi a gaban ‘yan jarida a kan shirun da ya yi a kotu.
Lauyoyi sun maida martani
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa lauyoyin da suka tsaya wa shehin sun musanya zargin da yake yi masu, suka kalubalance shi ya kai korafi inda ya kamata.
Rabiu Shu’aibu Abdullahi, a madadin sauran lauyoyin yace doka ba ta yarda ya fadi abin da ya faru tsakaninsu ba, amma yace za su iya daukar mataki a kansa.
Lafiyan Malamin kalau?
A zaman jiyan, kun ji cewa Likitan asibitin dawanau ya tabbatar da cewa, kwakwalwar Abduljabbar Nasiru Kabara,da Kuma kunnensa duk garau suke.
Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya daga zama sai ranar 30 ga watan Satumba, domin a kawo wasu lauyoyin.
Asali: Legit.ng