Abba Kyari, tsofaffin Gwamnoni da jerin wadanda ke tsare a gidan yarin Kuje
FCT, Abuja – Gidan gyaran hali da ke Kuje a birnin tarayya Abuja, ya na cikin manyan kurkukun da ake da su a Najeriya, yana cin dinbin mutane
A wannan rahoto, mun kawo sunayen wasu daga cikin shahararrun mutanen da ke tsare a gidan gyaran halin da aka kai wa hari a makon nan
Daga cikin wadanda ke tsare a kurkukun, akwai wadanda aka samu da laifi, akwai wadanda har yanzu ana shari’a da su, ba a yanke hukunci ba
Baya ga 'yan ta'addan Boko Haram, ga jerin wasu sunaye kamar yadda Daily Trust ta tsakuro wasu daga cikinsu, Legit.ng ta kara wasu a rahoton:
1. Abba Kyari
Babban jami’in ‘yan sanda DCP Abba Kyari wanda ya yi suna da ya rike rundunar IRT yana cikin wadanda ake tsare da su a wannan babban gidan yari.
Ana zargin DCP Abba Kyari da hannu wajen harkar saida kwayoyi. An shafe tsawon watanni uku kenan yana tsare, yayin da yake shari’a da NDLEA.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Joshua Dariye
Tun 2018 tsohon Gwamnan Filato, Joshua Dariye yake tsare a gidan gyaran halin bayan Alkalan kotun koli sun an same shi da laifin sata daga Baitul-mali.
Amma kwanakin baya aka ji Dariye yana cikin wadanda gwamnati ta yafewa laifuffukan da suka aikata, amma har a makon nan, ba a kai ga sakin shi ba.
3. Jolly Nyame
Shi ma Jolly Nyame tsohon Gwamnan Taraba ne wanda yake garkame a Kuje. A 2018 aka kama shi da laifin satar Naira biliyan 1.64 da wasu miliyoyin kudi.
4. Wadume
Wani mutumin Taraba a jerin shi ne Wadume Hamisu Bala wanda ake zargin ya yi kudi da garkuwa da mutane. Ana tuhumarsa da satar mutane da ta’addanci.
5. Abdulrasheed Maina
Sannan akwai Abdulrasheed Maina wanda ya jagoranci hukumar gyaran fansho na kasa, yana tsare yayin da ake EFCC ta ke shari’a da shi kan zargin satar N2bn.
6. Peter Nwachukwu
Peter Nwachukwu wanda ya auri Marigayiya Osinachi Nwachukwu ya na tsare a gidan yarin bisa zargin da ake yi masa na kashe mai dakinsa, mawakiyar coci.
7. Farouk Lawan
A gidan gyaran halin da ke garin Abuja ne Hon. Farouk Lawan yake tsare. A 2021 ne kotu ta samu tsohon ‘dan majalisar na Kano da laifin karbar cin hancin $500, 000.
An kai wa gidan yari hari
A yammacin Talata, 5 ga watan Yuli 2022 ne ku ka ji labari cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari a babban gidan gyaran hali na Kuje da ke cikin garin na Abuja.
Daga baya an tabbatar da cewa duka 'yan Boko Haram da ke tsare a gidan kason sun shirya. Ministan shari'a ya tabbatar da wannan labari a ranar Larabar nan.
Asali: Legit.ng