Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama

Majiya: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje sa'o'i 24 gabanin harin magarkama

  • Wasu majiyoyi sun bayyana abin da ya faru kafin aukuwar harin 'yan bindiga a magarkamar Kuje a Abuja
  • Majiyoyin sun ce, an kwashe sojojin da ke kewayen garin Kuje gabanin harin da kusan sa'o'i 24 na harin
  • Idan baku manta ba, a jiya ne aka samu mummunan faruwar harin 'yan ta'adda a babban binrin tarayya Abuja

Abuja - Majiyoyin tsaro, a ranar Laraba, sun bayyana cewa sojojin da aka tura yankin Kuje da kewayen magarkama, wadanda suka yiwa yankin farin sani, an sauya musu mazauni sa’o’i 24 kafin ‘yan ta’adda su kai hari gidan yarin Kuje.

Majiyar ta yi mamakin dalilin da ya sa aka kwashe su jami'an da suka san yankin sa'o'i 24 kafin harin, kuma har yanzu ba a samun wasu da suka maye gurbinsu ba har 'yan ta'addar suka far wa yankin, inji Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fallasa yan ta'addan da take zargi da kai hari Gidan Yarin Kuje

Yadda aka kwashe sojoji a kewayen Kuje gabanin harin 'yan bindiga
Rahoto: An kwashe sojojin da ke kewayen Kuje gabanin harin magarkama | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Sai dai kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wa'adin da ya kamata sojojin su zauna a wannan yankin ya wuce kuma dama ya kamata a sauya su.

Kamar yadda aka samo, majiyoyin tsaro sun shaidawa jaridar cewa ‘yan ta’addan sun samu nasarar doke shingayen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka dasa ta hanyar amfani da babura.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya ta ce a lokacin da ‘yan ta’addan suka so fara barnar, sai suka rika bude wuta da harsasai ratata, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka tsere wanda hakan ne a ba‘yan ta’addan hanyar aikata barnarsu.

Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista

Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce dukkan wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne a gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayya (FCT) sun tsere.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista

Ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron manema labarai a cibiyar da ke Abuja, inji rahoton TheCable.

Idabn baku manta ba, ‘yan bindiga sun kai hari gidan yarin, inda suka dasa nakiyoyi da ababen fashewa a daren ranar Talata.

Shuaib Belgore, sakataren dindindin na ma’aikatar harkokin cikin gida, ya ce maharan sun zo gidan yarin cikin “kyakkyawan shiri” dauke da bama-bamai.

An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Da alamu wasu manyan fursunoni a gidan yari na Kuje da ke Abuja sun tsere a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a daren ranar Talata, inji rahoton The Nation.

Harin da ya dauki tsawon sa'o'i kadan, an ce jami'an soji da masu gadin gidan yarin da ke bakin aiki sun yi artabu da tsagerun.

Majiyoyi sun ce mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari da abokan harkallarsa da ke wurin, mai yiwuwa sun tsere daga magarkama.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel