Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya buƙaci shugaba Buhari ya yi murabus

Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya buƙaci shugaba Buhari ya yi murabus

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC ya buƙaci shugaban kasa Buhari ya yi murabus duba da taɓarɓarewar tsaro a ƙasa
  • Dumebi Kachikwu ya ce tagwayen hare-haren da aka kai cikin awanni 24 sun fallasa ainihin raunin tsarin tsaron ƙasar nan da Buhari ya gaza ƙarfafa wa
  • A cewarsa idan har za'a kai wa Ayarin shugaban kasa hari da wuri kamar Kuje a Abuja to babu wanda yake tsare

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Dumebi Kachikwu, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi murabus saboda tabarɓarewar tsaro a sassan ƙasar nan.

A wata sanarwa da jaridar Vanguard ta rahoto, Kachikwu ya ce farmakin da mahara suka kai wa ayarin motocin shugaban da masu hidimta masa, da harin gidan Yarin Kuje, alamu ne a fili da ke nuna barazanar da ke dunfaro kasar nan.

Kachikwu da shugaba Buhari.
Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya buƙaci shugaba Buhari ya yi murabus Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewar ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya, waɗan nan hare-haren guda biyu manyan alamu ne da ke tabbatar da cewa Najeriya na cikin ƙalubalen tsaro mai muni.

Haka nan kuma ya nuna mamaki da Al'ajabin cewa idan har za'a farmaki ayarin motocin shugaban kasa da kuma gidan gyaran Hali kamar na Kuje, wanda ke da kilomita kaɗan zuwa Hedkwata, to wa kuma ya rage?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsarin tsaron Najeriya ya yi rauni - Kachikwu

Kachikwu ya ce waɗan nan tagwayen hare-haren da ƴan bindiga suka kai sun sake falƙasa asirin tsarin tsaron ƙasar nan, wanda shugaba Buhari ya gaza ƙarfafa shi.

A sanarwan Kachikwu ya ƙara da cewa:

"Abubuwan da suka faru awanni 24 nan baya da suka shuɗe sun ƙara tona asirin rashin ƙarkon tsarin tsaron ƙasar nan."
"An farmaki wasu mambobi na tawagar shugaban kasa yayin da aka kai hari gidan gyaran Halin Kuje da ke babban birnin ƙasar mu kuma aka kwance yan ta'adda suka tsere."

"Ina jajantawa iyalan waɗan da suka rasu kan aiki. Ina ƙara kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, cikin ruwan sanyi ya yi murabus tunda ba zai iya kare rayukan ƴan Najeriya ba."

A wani labarin kuma 'Ba zata saɓu ba' Jam'iyyar APC ta tashi tsaye, ta fara shirin dakile sauya shekar wasu mambobinta zuwa PDP

Alamu sun nuna uwar jam'iyyar APC ta tsoma baki domin shawo kan rikicin da ke kwashe mata 'ya'ya a jihar Kebbi.

Jam'iyya mai mulki ta kira taron masu ruwa da tsaki da mambobin da ran su ya ɓaci domin tattauna wa da kuma yin sulhu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel