Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Ziyarci Gidan Yarin Kuje Bayan Harin 'Boko Haram'
- Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara gidan yarin Kuje da ke Abuja inda wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari
- Usman Baba, Sufeta Janar na yan sanda, da Haliru Nababa, Kwantrola Janar na hukumar kula da gidan gyaran hali ne suka yi wa Buharin rakiya
- Bashir Magashi, Ministan Tsaro ya ce akwai wasu da ake zargin yan Boko Haram ne kimaninsu 64 a gidan yarin kuma an neme su an rasa
FCT Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Yan bindiga sun kai harin ne da abubuwa masu fashewa a daren ranar Talata.
Wani mazaunin unguwar Kuje ya shaidawa The Cable cewa sun ji karan harbin bindiga na kimanin mintuna 30 hakan ya jefa su cikin tashin hankali.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan gyaran halin.
Shugaban kasar, wanda a halin yanzu ya ke duba wurin, zai tafi Dakar, Senegal, anjima a yau.
Sufeta Janar na yan sanda da shugaban NCoS sun yi wa Buhari rakiya
Sufeta Janar na yan sanda, Usman Baba, da kwantrola Janar na hukumar kula da gidan gyaran hali, NCoS, Haliru Nababa sun yi wa Buhari rakiya.
Tun da farko, Bashir Magashi, ministan tsaro, ya ce yan Boko Haram ne suka kai harin.
Ya ce ba a ga mambobin Boko Haram 64 da ke gidan yarin ba.
"Sun taho da yawa sun saki wasu daga cikin yan gidan yarin," in ji shi.
"Muna kokarin ganin yadda za mu ga mun dawo dukkan wadanda suka tsere daga gidan yarin.
"Kimanin fursunoni 994, muna da 600 a ciki yanzu. An kamo wasu da dama. Mutanen da suko zo suka aikata wannan abin yan wata kungiya ce, bisa alamu yan Boko Haram ne.
"A halin yanzu mun kasa gano inda suke. Dama muna tsare da kimanin 64 ne kuma yanzu mun neme su mun rasa."
Dakaci karin bayani...
Asali: Legit.ng