Katsina: 'Yan ta'adda sun halaka mataimakin kwamishinan 'yan sanda tare da jami'i 1
- 'Yan ta'adda a karamar hukumar Dutsin Ma ta jihar Katsina sun halaka mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Aminu Umar, a ranar Talata
- Kwamandan yankin tare da wasu jami'ai sun kai dauki ne yayin da wasu masu ababen hawa suka sanar da su 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Zakka
- Sun yi nasarar halaka wasu daga cikin 'yan bindigan, amma wasu dake kan bishiya a boye sun harbe zakakurin 'dan sandan 'dan asalin garin Dabai ta Danja
Katsina - 'Yan bindiga sun halaka kwamandan 'yan sanda, Aminu Umar, a Dutsin Ma dake jihar Katsina a wani farmakin kwanton bauna da suka kai a safiyar Talata.
Umar, wanda mataimakin kwamishinan 'yan sanda ne, ya rasu tare da wani jami'in dan sanda daya.
Majiyoyi daga iyalinsa sun sanar da Premium Times cewa, an mika musu gasar Umar har garinsu dake Dabai a karamar hukumar Danja ta jihar Katsina a safiyar Laraba domin jana'iza.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya tabbatar da rasuwar Umar da dayan jami'in a wata takardar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani mazaunin Safana mai suna Lawali Shamsu, yace wasu masu ababen hawa ne suka sanar da jami'an 'yan sandan cewa sun ga wasu 'yan bindiga a kan babura suna tunkarar al'ummar Zakka dake karamar hukumar Safana ta jihar.
"A rashin sanin 'yan sandan, 'yan bindigan sun raba kansu gida biyu. Wasu daga cikinsu sun shiga kauyen yayin da wasu suka tsaya daga waje domin dakile taimakon jami'an tsaro," yace.
Ya ce 'yan sandan sun halaka 'yan bindiga masu yawa amma kuma jami'ai biyu sun rasa ransu sakamakon harbin da 'yan bindigan dake kan bishiya suka yi musu.
The Nation ta ruwaito cewa, duk da bai bada karin bayani kan yadda aka kashe kwamandan 'yan sandan ba, Isa yace 'yan bindigan sun fi dari uku dauke da makamai.
Yace jami'an sun je kakkabe daji ne lokacin da aka kashe su.
"Kwamandan yanki kuma daya daga cikin zakakuran 'yan sanda ya rasa rayuwarsa yayin da suka yi musayar wuta da 'yan bindiga," yace.
Premium times ta ruwaito cewa, Umar ba shi ne babban jami'in dan sanda da 'yan bindiga suka fara kashewa ba a cikin shekarar nan a Katsina.
A watan Fabrairun, DSP Abdullahi Rano ya rasu a wani harin kwanton bauna da aka yi musu yayin da yak jagorantar jami'ai don dakile farmaki a garin Magama Jibia.
'Yan bindiga sun sake sace wani babban fasto a Kaduna
A wani labari na daban, 'yan ta'adda a sa'o'in farko na ranar Litinin sun sake yin garkuwa da wani limamin cocin katolika, Rabaren Fada Emmanuel Silas a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Shugaban Catholic Diocese ta Kafanchan, Rabaren Fada Emmanuel Uchechukwu Okolo, ya tabbatar da hakan a wata takardar da ya bai wa manema labarai a Kaduna, jaridar Leadership ta ruwaito.
Idan za a tuna, 'yan ta'adda sun halaka Rabaren Fada Vaishima Barogo a gonarsa dake Kujama, kan babban titin Kaduna zuwa Kachia a ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2022 kuma an birne shi a ranar 30 ga watan Yunin 2022.
Asali: Legit.ng