Yau ‘Yan ta’adda za su fara yanka fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ke hannunsu

Yau ‘Yan ta’adda za su fara yanka fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ke hannunsu

  • Wani faifai yana yawo da aka ji fasinjan jirgin kasan Kaduna-Abuja yana kukan halin da suke ciki
  • Wannan mutumi da ke tsare a hannun miyagun ‘yan ta’adda, ya ce an fara maganar za a yanka su
  • Tukur Mamu ya tabbatar da ingancin sautin, yake cewa ‘yan ta’addan sun bada wa’adi zuwa yau

Kaduna - ‘Yan ta’ddan kungiyar Ansaru da suka tare jirgin kasan Abuja-Kaduna kwanaki, suka dauke fasinjoji, su na barazanar kashe wadanda su ke tsaren.

Rahoto ya fito daga Daily Trust cewa ‘yan ta’addan sun yi magana cewa idan ba a biya masu bukatunsu ba, za su dauki fansa a kan wadanda suka kama.

Wani sakon sauti yana yawo a halin yanzu, a ciki aka ji wani a cikin wadanda ‘yan kungiyar ta Ansaru suka rike, yana cewa za a yanka sauran da ke tsare.

Kara karanta wannan

Wanda aka yi a idonsa, ya bada labarin yadda Miyagu suka aukawa Ayarin Shugaban kasa

Wannan mutumi yake cewa tun da har gwamnatin tarayya ba ta biyawa ‘yan ta’addan bukatunsu ba, sun dawo ta kan su, su na barazanar cewa za su yanka su.

Haka aka yi – Tukur Mamu

Tukur Mamu ya tabbatar da ingancin fai-fen, ya kuma ce shakka babu, ‘yan ta’addan sun zabi yau (Laraba) a matsayin ranar da za su soma wannan danyen aiki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhaji Tukur Mamu yana cikin wadanda suka zama sila tsakanin gwamnati da ‘yan ta’addan.

Jirgin kasa
Jirgin kasan Abuja-Kaduna
Asali: UGC

Mamu ya shaidawa Daily Trust cewa shi ya roki ‘yan ta’addan da su yi hakuri, su nemi bukatunsu a wajen ‘yanuwan wadannan Bayin Allah da suke hannunsu.

Bayan Mamu ya nemi alfarma, sai suka bukaci ayi hakan ganin cewa gwamnati ta na bata lokaci. Amma sun ce idan suka ji shiru a nan ma, za su fara kashe su.

Kara karanta wannan

Adadin wadanda aka kashe a Shiroro ya kai 48, ciki akwai Soji 34: Inji shugaban matasan yankin

Yadda Mamu ya yi da su

“Mutanen nan sun harzuka a ranar Litinin, bayan sun bamu wata dama. Nayi kuka, ina rokonsu cewa tun da gwamnati ta na bata lokaci, me zai hana su tattauna kai-tsaye da ‘yanuwan wadanda suka kama, sai a sasanta.”
“Bayan na roke su, sun yarda cewa za su yi magana kai-tsaye da ‘yanuwan mutanen da suka dauke.”
“Amma sun ce sun bamu har zuwa Laraba, idan ba su ji komai daga wajen wadanda suke so a sasanta ba, za su fara yanka wasu cikin wadanda suka kama.”

- Tukur Mamu

An tare jirgi ya na hanya

A ranar Talata, 29 ga watan Maris 2022, ku ka samu labari cewa Rotimi Amaechi, a lokacin yana Ministan sufuri, yace ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin.

Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe N3bn wajen sayan wasu kayan tsaro, ya ce rashin tanadar wadannan kayan aiki, ya sa aka iya kai harin.

Kara karanta wannan

Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'un a zabe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng