Muhimman Abubuwa 8 da ya kamata a sani game da Dr Muhammad Barkindo

Muhimman Abubuwa 8 da ya kamata a sani game da Dr Muhammad Barkindo

A ranar Talata, 5 ga watan Yulin 2022 ne Allah yayi wa sakatare janar na Kungiyar kasashe masu fitar da man fetur, OPEC, Muhammad Sanusi Barkindo rasuwa.

Rasuwarsa ta zo kwatsam a lokacin da yake da shekaru 63 a duniya. Ga wasu muhimman abubuwan da ya dace a sani game da shi:

Dr Muhammad Sanusi Barkindo
Muhimman Abubuwa da ya kamata a sani game da Dr Muhammad Barkindo. Hotodaga thisdaylive.com
Asali: UGC

  1. An haife shi a garin Yola dake jihar Adamawa a ranar 20 ga watan Afirilin 1959 kuma ya rasu a ranar 5 ga watan Yulin 2022, wanda hakan yake nufin ya rasu yana da shekaru 63 a duniya.
  2. Muhammad Sanusi Barkindo yayi digirinsa na farko a fannin siyasa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria kuma ya kammala a shekarar 1981.
  3. Ya yi dufuloma a fannin tattalin arziki na man fetur shekarar 1988 a jami'ar Oxford.
  4. Ya yi digirin digir a fannin kasuwanci a jami'ar Washington a shekarar 1991.
  5. An karrama shi da digirin digirgir daga jami'ar Fasaha ta tarayya dake Yola.
  6. Dan siyasar ya kwashe shekaru 24 yana aiki da NNPC inda har ya kai matakin GMD.
  7. Kafin rasuwarsa, ya haye kujerar sakatare janar na OPEC a ranar 1 ga watan Augustan 2016.
  8. Barkindo na son karatu, ayyukan taimako, duk abinda ya shafin muhalli da kuma kwallon kafa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Bayan sa'o'i kadan da ganawa da Buhari, Sakatare janar na OPEC ya rasu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Allah ya yi wa Muhammad Barkindo, sakatare janar na OPEC, rasuwa

A wani labari na daban, Muhammad Sanusi Barkindo, sakataren janar na Kungiyar Kasashe masu fitar da man fetur, ya rasu. Mele Kyari, manajan daraktan Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC, ya bada sanarwar mutuwarsa a wallafarsa ta Twitter a sa'o'in farko na ranar Laraba.

Kyari yace ya rasu wurin karfe 11 na daren Talata, yana da shekaru 63 a duniya. Ya kwatanta rasuwarsa da babban rashin ga iyalnsa, NNPC Najeriya, OPEC da duniya baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng