Darakoci 20 ke rige-rigen maye gurbin korarren Akanta Janar

Darakoci 20 ke rige-rigen maye gurbin korarren Akanta Janar

  • Gwamnatin tarayya na shirye-shiryen nada sabon akanta janar na tarayya, kuma zata zaba ne a daya daga cikin daraktoci kuma akantocin gwamnati
  • Daraktocin da suka kai mataki na 17 a aikin gwamnati kafin 1 ga watan Janairu 2020 kuma wadanda ba za suyi ritaya kafin 31 ga watan Disamba 2024 ne kadai ke da damar shiga gasar
  • Wata majiya da ba a tabbatar da sahihancinta ba ta tabbatar da yadda sama da daraktoci 20 suka shigar da bukatar darewa kujerar bayan sallama sabon akanta da aka yi

FCT, Abuja - Gwamnati tarayya ta fitar da takardar shirye-shiryen nada sabon akanta janar na tarayya, The Punch ta gano hakan.

Dr Folasade Yemi
Darakoci 20 ke rige-rigen maye gurbin korarren Akanta Janar. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A takardar da ta fita ranar 21 ga Yuni, 2022 daga ofishin shugaban ma'aikatan gwamnati na tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, gwamnatin tarayya ta ce, "Bayan amincewar shugaban kasa, ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ya fara kokarin ganin an nada sabon akanta janar na tarayya daga daraktocin da suka cancanta don zama akanta janar na tarayya."

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: ASUU ta kafawa FG sharudda 2 tak, tace ana cikasu gobe za a koma karatu

Mukamin, kamar yadda takardar da The Punch ta samu, na wadanda suka kai matakin darakta ko matakin albashi na 17 a ranar ko kafin ranar 1 ga watan Janairu 2020 ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyoyi a ma'aikatar kudi sun bayyana yadda sakatarai na dindindin suka mika jerin sunayen daraktocin da suka cancanta, don mukamin.

Haka zalika, an ango yadda daraktocin ke tururuwar ganin sun shiga jerin sunayen wadanda za a zaba a matsayin AGF.

Wata majiya da ba a tabbatar da sahihancinta ba ta bayyana yadda a kalla daraktoci 20 suka shigar da bukatar kujerar.

Sai dai, The Punch bata samu damar tabbatar da hakan ba yayin da kakakin akanta janar na tarayya, Henshaw Ogubuike, bai amsa kiraye-kirayen waya ba balle ya maida amsar sakon kar ta kwanan da aka tura masa.

Haka zalika, takardar mai taken, "Cigaba da kokarin ganin an nada wanda ya cancanta ya rike mukamin akanta janar na tarayya, wacce ta kunsa dukkan akawuna da ke aikin gwamnati sannan suke son darewa kujerar akawu-janar na tarayya dole su kasance sun kai matakin darakta (albashi mataki na 17) a rana ko kafin 1 ga watan Janairu 2020 kuma ba za su yi ritaya kafin 31 ga watan Disamba 2024 ba, za su iya shiga gasa.

Kara karanta wannan

PDP ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tuhumi Buratai kan kudin makamai

"Sai dai an cire ma'aikatan da ke kan ladubban ladabtarwa daga gasar. Ana bukatar sakatarai na dindindin da su tura abubbuwan nan: jerin sunayen daraktocin SGL. 17; bayanan sirri da fayel din dukkan daraktocin da suka cancanta; kwafi biyar na CV na kowanne darakta; bayanan kowanne daraktan a. Za a tura shi ga adireshin yanar gizo na ohcsfemd@ohcsf.gov.ng."
Ya kara da cewa, "Takarda a sakin layi na hudu da ke sama dole ta isa ofishin sakataran dindindin, ofishin kula da ayyuka, ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin na tarayya, Block A, 4th Floor, Sakateriyar tarayya, Phase II a ranar ko kafin karfe 4:00 na yammacin Laraba, 6 ga watan Yuli, 2022. Da fatan zaku bayyanar da abun da wannan takardar ta kunsa ga dukkan wadanda ta shafa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel