Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP, Sun Raunata Mambobi Sun Kona Motocci Da Babura A Jihar Arewa

Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP, Sun Raunata Mambobi Sun Kona Motocci Da Babura A Jihar Arewa

  • Wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari wurin da matasan jam'iyyar PDP ke taro a Ologba, Karamar hukumar Dekina, Jihar Kogi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an raunata a kalla mutane 10, an kuma kona babura da motocci na mambobin na PDP
  • Jam'iyyar ta PDP ta yi Allah wadai da harin ta kuma ce ba za ta lamunci a cigaba da kaiwa mambobinta hari ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kogi - A kalla mutane 10 ne suka jikkata bayan wasu da ake zargin yan daba ne suka kai hari wurin taron matasan jam'iyyar PDP a Ologba a karamar hukumar Dekina, Jihar Kogi.

Wani ganau ya shaidawa wakilin The Punch a ranar Talata cewa yan daban sunyi amfani da bindigu, wukake, kaho da wasu abubuwa masu hadari yayin harin.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun jikkata yayin da yan daba suka farmaki taron PDP a Kogi

Taswirar Jihar Kogi
Yan Daba Sun Tarwatsa Taron PDP, Sun Raunata Mambobi Da Dama a Jihar Kogi. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

An gano cewa bata garin sun kuma kona motocci da baburan wasu yan PDP kuma sun kona gidan shugaban matasa na PDP a Iyale.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ana zaman dar-dar a karamar hukumar Dekina. Yan daban sun zo wurin da matasan PDP ke taro a jiya a Ologba, suka lalata kayayyaki, suna kona motocci da babura," daya cikin majiyoyin ya ce.

Martanin jam'iyyar PDP a Kogi

A bangarenta, jam'iyyar PDP ta jihar Kogi ta yi tir da harin da aka kaiwa mambobinta.

Jam'iyyar ta ce ba za ta lamunci kai wa mambobinta hare-hare ba kamar yadda aka saba.

Jam'iyyar, cikin sanarwa da Dayo Onibayo, direktan watsa labarai ya rattaba wa hannu ta yi gargadi kan kai wa mambobinta hari kuma ta ce za ta bari yan sanda su kammala bincike kafin ta dauki mataki.

Kara karanta wannan

Tonon sililin PDP: Akwai babbar magana a 2023, APC ta shirya siyan kuri'un a zabe

PDPn ta kuma yi kira ga mambobina su kwantar da hankalansu duk da neman tunzura su da ake yi.

2023: Idan Har Ka Ajiye Okowa, Ba Zaka Samu Kuri'an Igbo Ba, Matasan Ohanaeze Sun Gargadi Atiku Da PDP

A wani rahoton, matasan Igbo karkashin kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council Worldwide, OYC, ta gargadi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar kan duk wani shiri na ajiye Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

A cikin da shugabannin kungiyar suka raba wa yan jarida a ranar Talata, ta ce idan Atiku ya ajiye Okowa, duk abin ya faru, shi ya janyo, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel