Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi

  • Jarumar fim din da ta auri musulmi ta jawo cece-kuce a shafin Instagram yayin da ta ce za ta iya musulunta
  • Ta bayyana cewa, shiga irin ta musulmai na mata matukar kyau, kuma hakan yana matukar ba ta sha'awa
  • Mutanen da ke bibiyar ta a shafin Instagram sun yi martani, sun bayyana irin abin da suka ji game da hakan

Jarumar fina-finan Najeriya da suka shahara da Nollywood, Mercy Aigbe ta bayyana cewa za ta iya zama Musulma, kuma hakan ba komai bane.

Aigbe ta fadi haka ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da take bayyana yadda take jin dadin sabon salon shigar ta.

Mercy Aigbe ta ce za ta iya muslunta
Shigar musulmai na burgeni, zan iya muslunta, inji 'yar fim Mercy Aigbe da ta auri Musulmi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Jarumar dai ita ce mata ta biyu ga wani dan kasuwar harkar fina-finai, Kazim Adeoti wanda aka fi sani da Adekaz.

Jarumar ta rubuta a shafinta na Instagram cewa:

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba karya, ina jin dadin wannan sabuwar shiga ta Hajiya. Zan iya zama Alhaja a zahiri. Abin yana min dadi, amma dai akwai wahala! A karshe dai, muna bauta wa Allah daya.”

Martanin 'yan Instagram

Mabiyanta a kafar Instagram sun yi martani game da ganinta cikin wannan sutura, da kuma maganar da ta yi a kai.

@youngwealth_042:

"Ranki ya dade kinyi kyau sosai, ina nuna matukar so da girmamawa."

@hibahworld:

Zai yiwu, duk abinda Allaah ya sauwaka sai ya zama mai sauki. Kina iya zama da gaske."

@memumsister:

"Hanya daga Hajia zuwa Alhaja na da kyau 'yar uwa, Hajjin 2023 na kiranki."

@ra_mensworld:

"Bama bautawa Allah daya!! A saukaken harshe, ba za su ce abu daya ba."

@bishi4ril:

"'Yar uwata dan Allah kar a yaudaru Yesu Ubangiji ne, dawwama shine babban abin da ake mayar da hankali akai. Kyakkyawa ce ke kuma ni mai bibiyarki ce amma don Allah kar ki bar Kiristi."

Kara karanta wannan

Abin na yi ne: Za a dauki mutane miliyan 1 aiki a 2023 domin gano yawan 'Yan Najeriya

'Yar jarida Stella ta caccaki Kemi bisa zarginta da kulla soyayya da Fani Kayode a can baya

A wani rahoton GistLover, Fitacciyar 'yar jaridar nan 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Jamus, Stella Dimoko Korkus ta yi kira ga Kemi Olunloyo ta nemi lashe amanta kan wani batu, bayan da tsohon minista sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode da matarsa, Precious Chikwendu suka sasanta tsakaninsu.

A 2020, lokacin da Femi Fani Kayode da Precious Chikwendu ke kai ruwa rana game da makomar ‘ya’yansu, Kemi Olunloyo ta zargi Stella Dimoko Korkus da kulla soyayyar wucin gadi da Fani Kayode a shekarun da ya gabata.

Stella, wacce a baya bata taba cewa uffan kan zargin ba, a karshe dai ta magantu bayan da Fani Kayode da Precious suka sasanta rikicin da suke na tsawon shekara biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.