Hajjin bana: Tashi ya gagara, alhazan Neja 2,265 sun shiga zulumi da takaici

Hajjin bana: Tashi ya gagara, alhazan Neja 2,265 sun shiga zulumi da takaici

  • Alhazai a jihar Neja sun makale kwanaki biyu gabanin rufe filin jirgin sama na Jeddah a kasar Saudiyya
  • Wannan na zuwa ne saboda tsaikon da aka samu na jigilar maniyyata aikin Hajjin bana a jihar kamar yadda majiya ta shaida
  • A cewar wasu da alamarin ya shafa, ba su ji dadin yadda hukumomin tafiyar ke tafiyar lamurran tashin su ba

Jihar Neja - Sama da maniyyata aikin hajjin jihar Neja 2,265 da yanzu za su tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe Abuja maimakon filin jirgin sama na Minna kamar yadda aka tsara tun farko ke koka yadda hukumomi ke tafiyar da al’amuransu.

Leadership ta ruwaito cewa maniyyatan sun makale ne a sansanin alhazai na Tundun Fulani da ke karamar hukumar Bosso a jihar na tsawon kwanaki suna jiran a tashi dasu daga filin jirgin Minna.

Kara karanta wannan

Duk daya muke: Kristoci sun taya musulmai cire ciyayi a masalacin Kaduna.

Yadda maniyyata ke tagumi kan rashin tashin jirgi
Hajjin bana: Tashi ya gagara, alhazan Neja 2,265 sun yi tagumi yayin Sallah ke matsowa | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wasu daga cikin maniyyatan da suka zanta da jaridar sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake tafiyar da lamurransu zuwa yanzu, sun kuma dora laifin matsalar ga karancin jiragen da aka ware wa jihar.

Fusatattun maniyyatan sun ce ba a sanar da su gaskiya game da hakikanin halin da jirgin ke ciki, kuma sun koka kan yadda babu wani da aka tafi dashi kasa mai tsarki kwanaki biyu gabanin wa'adin rufe filin jirgin Jeddah na kasar Saudiyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Umar Makun Lapai ya tabbatar wa jaridar tsaikon da aka samu na jigilar alhazai daga jihar.

Ya ce:

“Tuni yanzu dai muna kan hanyarmu ta zuwa filin jirgin Abuja tare da alhazai 560 daga cikin 2,265 da suka fito daga jihar domin fara jigilar fasinjoji zuwa Saudiyya.”

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Da aka tambaye shi game da jigilar alhazai daga filin jirgin Minna, sai ya ce:

“Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ce ke rabon jiragen kuma jihar na bin ka'ida ne kawai."

Saudiyya ta tsawaita wa'adin saukar jiragen Najeriya a Jeddah

Yayin alhazai ke koka karatowar wa'adin saukar jirage a Saudiyya, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta GACA a kasar Saudiyya ta tsawaita izinin sauka daga ranar 4 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Yuli na alhazan Najeriya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakiyar darakta a sashen hulda da jama’a na hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Fatima Usara ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja.

Ta bayyana cewa ya zama dole ne a tsawaita wa’adin tashi da saukar jiragen sama saboda tsaikon da jirge suka samu.

Hajjin bana: Lokaci yana nema ya kure, har yanzu ba a dauki 50% na Maniyyatan Najeriya ba

Kara karanta wannan

INEC ta bayyana damuwarta akan karancin rajistar katin zabe a jihar Katsina

A wani labarin, kwanaki kadan suka rage a kammala jigilar maniyyatan wannan shekara zuwa kasa mai tsarki, amma har yanzu mutanen Najeriya su na gida.

Daily Trust ta ce daga cikin mutane 43, 000 da suka biya kudin aikin hajjin shekarar bana, wadanda aka dauka zuwa Saudi ba su kai rabi ba.

Har zuwa ranar Talata, 28 ga watan Yuni 2022, alkaluman hukumar kula da Alhazai ta NAHCON ta tabbatar da cewa maniyyata 19, 764 kurum suka isa Saudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.