Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa

Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Angwan Baraya da ke masarautar Pyem a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau
  • Maharan sun raunata hakimin garin, Baba Yarima Jabil sannan suka harbe dansa tare da yin awon gaba da matarsa da wata
  • Rundunar yan sandan jihar bata tabbatar da lamarin ba zuwa yanzu inda kakakinta ya ce bai samu rahoto kan lamarin ba tukuna

Plateau Tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Angwan Baraya da ke masarautar Pyem, karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau inda suke ta harbi kan mai uwa da wahabi.

A yayin harin wanda ya afku a safiyar Lahadi, 3 ga watan Yuli, yan bindigar sun raunata hakimin garin, Baba Yarima Jabil sannan suka harbe dansa mai suna Chamsan har lahira.

Yan bindiga
Yan bindiga sun yi garkuwa da matar wani basarake a Plateau, sun kashe dansa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, maharan sun yi awon gaba da matar hakimin da kuma wata kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Peter Obi bashi da tsaurin ra'ayin addini kuma baya kyamar mutanen Arewa

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa an yi gaggawan daukar hakimin garin zuwa wani asibitin yankin inda al’ummar yankin suka cika da damuwa kan hare-haren da yan bindiga ke kaiwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rundunar yan sandan jihar bata tabbatar da lamarin ba har yanzu yayin da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Alfred Alabo, ya ce bai samu kowani rahoto daga shugaban yan sandan yankin ba.

Sai dai kuma, wani mazaunin yankin, Audu Ibrahim ya ce yan bindigar sun zo ne a tsakar dare sannan suka farmaki gidan hakimin garin, suna ta harbi kan mai uwa da wahabi yayin da mazauna suka tarwatse don neman mafaka.

Ya ce:

“Sun kasance dauke da muggan makamai duba ga karar harbi da muka dungi ji, sun san inda suka dosa domin sun farmaki gidan Baba Yarima Jabil ne. Maharan sun harbe shi. Da nutsuwa ua dawo yankin, mun gano cewa yana da rai don haka aka kwashe shi zuwa asibiti amma dansa, Chamsan bai taki sa’a ba domin an gano shi a mace.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Mun Fara Kare Kanmu A Birnin Gwari, In Ji Shugaban Al'umma a Kaduna

“Yan bindigar sun yi awon gaba da mata biyu kuma daya daga cikinsu matar hakimin ne. Basu kira ba tukuna amma mun damu da lamarin saboda mun zama marasa galihu. Da abun ya faru, an kira jami’an tsaro amma sun zo ne bayan aikin gama ya gama sannan maharan sun bar garin.”

Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

A wani labarin, mun ji cewa akalla al'ummomi 30 ne 'yan bindiga suka tasa a matsugunansu a yankunan jihar Zamfara a cikin wata daya, inji dan majalisar tarayya mai wakilar Gummi/Bukkuyum, Suleiman Abubakar Gumi.

Jigon na siyasa ya bijiro da batun ne a yayin gabatar da wani kudiri kan bukatar kara yawan jami'an sojoji ga yankunan da abin ya shafa a jihar domin ganin karshen matsalolin da ke ta'azzara.

A cewar Gumi, ‘yan bindiga sun farmaka wasu al’ummomi a jihar, inda suka hallaka akalla mutane 16, tare da jikkata wasu da dama.

Kara karanta wannan

Sojoji da Mafarauta sun Halaka tare da Damke Wasu 'Yan Ta'adda a Jihohin Kaduna da Filato

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng