Yan Bindiga: Mun Fara Kare Kanmu A Birnin Gwari, In Ji Shugaban Al'umma a Kaduna

Yan Bindiga: Mun Fara Kare Kanmu A Birnin Gwari, In Ji Shugaban Al'umma a Kaduna

  • Zubairu Idris Abdulrauf, jagoran al'umma a karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna ya ce mutanen garinsu sun fara kare kansu daga yan bindiga da ke kawo musu hari
  • Abdulrauf ya ce mutanen yankin sun dade suna zaman kunshi karkashin yan bindiga suna biyan haraji kuma jami'an tsaro ba su musu maganin yan bindigan ba
  • Tsohon manajan na KSMC ya ce ya goyi bayan umurnin da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya bawa mutanen jiharsa da su mallaki makamai su kare kansu

Kaduna - Saboda hare-haren yan bindiga a masarautar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, jagoran al'umma kuma tsohon manajan KSMC, Alh. Zubairu Idris Abdulrauf, ya yi maraba da umurin da gwamnan Zamfara ya yi na cewa mutane su kare kansu, yana cewa tuni mutanen masarautar sun rungumi tsarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Abdulrauf cikin wata hira da aka yi da shi kan hare-haren yan bindigan ya janyo rushewar kasuwanci da tattalin arziki a yankin kuma wasu wuraren ba su shiguwa, rahoton Vanguard.

Zubairu Idris Abdulrauf
Yan Bindiga: Mun Fara Kare Kanmu A Birnin Gwari, In Ji Jagoran Al'umma. @VanguardNGA.
Asali: Twitter

A cewarsa, "An kai mu karshe. Mutane sun gaji. Jiya, Randegi daya daga cikin wurare ne da yan bindiga ke da hanyarsu zuwa Jihohin Zamfara a Niger."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jiya, mutanen Randegi sunyi fito na fito da yan bindiga da suka so mamaye Randegi, garin manoma, kuma sunyi nasarar fatattakar yan bindigan. Don haka, ina tunanin mutanen mu sun shirya idan gwamnati bata shirya yin aikin da kundin tsarin mulki ya dora mata ba."
Tsohon mai watsa labarai da gidan rediyo na DW din ya ce tsawon shekaru 2, yan bindigan sun saka wa manoman Birnin Gwari haraji, yana mai cewa:
"Eh, an biya yan bindigan Naira miliyan 200 a mazabar Randegi kawai."

Kara karanta wannan

Zamfara: Kanal Dangiwa Ya Bayyana Hatsarin Da Ke Tattare Da Mallakawa Mutane Bindiga, Ya Bayyana Mafita

"Idan ka yi maganan karamar hukumar Birnin Gwari baki daya, an biya yan bindigan tsakanin Naira miliyan 300 zuwa 400."

Haraji iri uku manoman Birnin Gwari ke biyan yan bindiga

Ya cigaba da cewa harajin ma iri uku zak, biya:

"Kafin fara noma, tsakiyar damina da kuma lokacin da kayan gona suka fara yaya. Idan baka biya ba ba za su bari ka shiga gonarka ba. Sannan idan an kammala noma za ka biya haraji kafin su bari ka shiga gonarka.
"Kuma bayan ka shiga gonarka bayan biyan harajin, za su fada maka bayan biyansu kudi, za ka basu buhu 2 cikin kowanne 10 na hatsin da ka noma."

Shekaru uku da suka gabata, halin da manoman Birnin Gwari ke ciki kenan kuma idan mutane sun shiga irin mummunan damuwa, za su nemi mafita shine su kare kansu idan gwamnati ta gaza kare su.

"Idan ba a dauki mataki ba, za mu samu matsar abinci. Birnin Gwari ta saba noma ton 700 na hatsi amma yanzu mutane ba su iya zuwa gonakinsu," in ji shi.

Kara karanta wannan

A Shirye Nake In Jagoranci Yaki da 'Yan Bindiga a Jihata, Gwamnan Bauchi

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa

A wani labarin, kun ji cewa an yi garkuwa da basarake mai sanda mai daraja ta daya a jihar Kogi, Adogu na Eganyi a karamar hukumar Ajaokuta, Alhaji Mohammed Adembe kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace basaraken ne a ranar Talata a kan hanyar Okene zuwa Adogo, rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel