Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Alla-wadai da harin da 'yan bindiga suka kai wani yankin Neja
  • A makon nan ne aka samu aukuwar wani harin da ya yi sanadiyyar mutuwar jama'a tare da yin awon gaba da wasu
  • Buhari ya ce babu zama, dole a ceto su, kuma zai tabbatar da hukunta duk wani dan ta'adda da ya shiga komar hukuma

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Juma’a, ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an ceto wadanda aka sace a wani hari da aka kai a wani wurin hakar ma’adinai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Buhari ya fadi haka ne yate da bayyana harin a matsayin harin kai tsaye kan Najeriya masu bin doka da oda wanda ba za a bari ya tafi haka siddan ba.

Kara karanta wannan

Bata-gari: An kama 'yan mata 20 da samari 14 da ke rawar badala a jihar Gombe

Buhari ya yi Allah wadai da kashe jama'a a jihar Neja
Harin Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto wadanda aka sace, zai hukunta 'yan ta'adda | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wata sanarwa ta Juma’a mai dauke da sa hannun hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, shugaban ya kuma jinjina wa sojojin da suka rasa rayukansu wajen dakile harin yana mai cewa kokarinsu ba zai zama na banza ba.

Jaridar Punch ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sama da mutane 43 da suka hada da sojoji 30 da kuma ‘yan sandan mobal bakwai a harin da aka kai ranar Laraba. A cewar mazauna yankin, an kuma yi awon gaba da wasu ‘yan China da 'yan Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Nation ta ruwaito sanarwar na cewa:

“Muna girmama jami’an tsaron mu, musamman jajirtattun rayukan da suka sadaukar da kawunansu wajen yakar muggan ayyukan ta’addanci. Sun kasance mafi kyawun abin da Najeriya za ta bayar kuma muna tunawa da kowannensu."

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta rage tasirin Boko Haram da sauran kungiyoyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

Ya kuma ce, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da tsaron 'yan Najeriya, tare da hukunta 'yan ta'adda.

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

A wani labarin, a kalla rayuka 17 sun salwanta bayan wadanda suka samu matsanantan raunuka yayin da 'yan ta'adda suka kai farmaki mahakar ma'adanan da 'yan kasar Sin ke kula dashi tsakanin Ajata da Aboki cikin gundumar Gurmana na karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

An ruwaito yadda harin ya auku ranar Laraba da tsakar rana inda aka halaka mutane 17 duk da 'yan sandan da ke tsere mahaka ma'adanan da ma'aikata.

An gano yadda maharan suka yi dirar mikiya da miyagun makamai misalin karfe 2:00 na rana a anguwar, inda suka doshi wajan da ake hakin tare da budewa duk wanda suka yi tozali dashi wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.