Bidiyon Bahaushe gangaran a harshen Ibo ya girgiza intanet, ya sanyawa 'yarsa Ngozi

Bidiyon Bahaushe gangaran a harshen Ibo ya girgiza intanet, ya sanyawa 'yarsa Ngozi

  • Bidiyon wani Bahaushe da ke magana da harshen Ibo ya bazu a shafukan intanet inda ya jawo cece-kuce
  • Mutumin da ba a bayyana sunansa ba ya ce ya sanya wa 'yar sa suna Ngozi ne saboda kaunar da yake da shi da harshen Ibo
  • Jama’a da dama sun taru a wajensa a lokacin da ake hira dashi da harshen Igbo bayan da wani ya ba shi wasu kudi

Bidiyon da aka ga wani Bahaushe yana magana da harshen Ibo ya ja hankalin masu amfani da shafin yanar gizo a kwanan nan.

Bidiyon ya kuma janyo cece-kuce musamman yadda mutumin ya bayyana cewa ya sanya wa abin da ya haifa suna Ngozi saboda tsananin kaunar harshen Ibo.

Baushe ya ba da mamaki da yadda yake magana da harshen inyamuranci
Bidiyon Bahaushe gangaran a harshen Ibo ya girgiza intanet, jama'a sun sha mamaki | Hoto: @Themannnaman
Asali: Twitter

Ba a san asalin tushen bidiyon ba, amma an gan shi a wasu shafukan Twitter ciki har da na @Themannnaman.

Kara karanta wannan

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

A cikin faifan bidiyon, mutumin ya yi magana da yaren kamar wani gangaran, wanda ya ja hankalin masu wucewa, wasu daga cikinsu sun taru suna kallon ikon Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin ya bar wurin, wanda ke hira da shi ya ba shi wasu kudade ganin yadda ya burge ainun.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan Twitter

@kaizer747 ya ce:

"Gaskiya na zubar da hawaye yayin kallon wannan, 'yan siyasa sun yi mana matukar illa a matsayinmu na al'umma. Hadewar dunkulalliyar Najeriya mai yiwuwa ne idan muka kaucewa duk wani cece-ku-ce da kabilanci."

@Dan__Ismail yace:

"Wannan ba sabon abu bane dan uwa. Adadin Ibo masu jin Hausa a Arewa ya zarce Hausawa da ke Gabashi."

@thatanambrababe ya ce:

"Hausawa mutane ne masu ban al'ajabi! Na kasance tare da su, kuma na yi kasuwanci da su, suna da amana, kuma suna da yarda, matukar baka rushe wannan yardar ba. Suna da matukar son jama'a kuma ba sa jin tsoron cin abinci a faranti daya da kowa."

Kara karanta wannan

Bidiyon Cikin Tamfatsetsen Katafaren Otal dake Yawo a Sararin Samaniya Tamkar Tsuntsu

@GENERALKEN01 ya ce:

"Bayan komai da ya faru dan kabilar Ibon ya ba shi kudi, 'yan kabilar Igbo kenan, mun san yadda ake nuna soyayyar 'yan uwantaka ba tare da la'akari da inda ka fito ba."

'Yar jarida Stella ta caccaki Kemi bisa zarginta da kulla soyayya da Fani Kayode a can baya

A wani rahoton GistLover, fitacciyar 'yar jaridar nan 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Jamus, Stella Dimoko Korkus ta yi kira ga Kemi Olunloyo ta nemi lashe amanta kan wani batu, bayan da tsohon minista sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode da matarsa, Precious Chikwendu suka sasanta tsakaninsu.

A 2020, lokacin da Femi Fani Kayode da Precious Chikwendu ke kai ruwa rana game da makomar ‘ya’yansu, Kemi Olunloyo ta zargi Stella Dimoko Korkus da kulla soyayyar wucin gadi da Fani Kayode a shekarun da ya gabata.

Stella, wacce a baya bata taba cewa uffan kan zargin ba, a karshe dai ta magantu bayan da Fani Kayode da Precious suka sasanta rikicin da suke na tsawon shekara biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.