Bidiyon Cikin Tamfatsetsen Katafaren Otal dake Yawo a Sararin Samaniya Tamkar Tsuntsu
- Bidiyon yadda aka tsara wani tamfatsetsen Otel mai yawo a sararin samaniya wanda aka kera cikin fasaha ta yadda ba zai taba sauka kasa ba ya jawo cece-kuce a yanar gizo
- A cewar wanda ya kera mai suna Hashem Alghaili, Injinan hada nukiliya 20 ne za su iya rike otel din mai suna Sky Cruise na tsawon shekaru
- Sky Cruise ya kun shi cibiyar wasanni, gidan siyar da abinci, mashaya, wajen wasa, gidan kallon kwallo, dakin taron biki da duk wani abun more rayuwa
Wani mai shirya fina-finai kuma mai kera abubuwa mai suna Hashem Alghaili da wani mutum mai suna Tony Holmsten sun shirya bikin bude wani tamfatsetsen otel mai cike da ababen more rayuwa wanda ke yawo a sararin samaniya mai suna Sky Cruise.
Cikakken bidiyon otel din da @nypost ya wallafa a shafinta na Instagram ya matukar ba masu amfani da yanar gizo mamaki wanda ya jawo jerin tambayoyi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An kera Sky Cruise ne don ya cigaba da yawo a sararin samaniya har abada. A wani rahoto da NYPost suka samo, makerin otel mai ban mamaki Al-Ghaili ya yi imani da cewa cigaba ne na zirga-zirga.
Haka zalika, Al-Ghaili ya kara da bayyana cewa ba matuka jirgi bane ke tukashi. " Duk irin wannan fasahar sai an bukaci matuka jirgi? Nayi imani da otel ne mai matukar dogaro da kansa."
Sky Cruise din da ba a ambaci ranar da za a sakeshi ba don ya cigaba da yawo a sararin samaniya har abada. Cruise din da zai yi aiki da injinan hada nukiliya 20 zai bukaci ma'aikata da dama don kula da baki.
Ta otel din ana iya ganin gaba daya sararin samaniya, ya kunshi wajen shakatawa, dakin bikin aure, wajen iyo, dakin toro, wajen siyayya, cibiyar wasanni, gidan sai da abinci, gidan giya, filin wasan yara da gidan kallon kwallo.
Za a dauki fasinjojin shi gami da aje su a gidajensu.
Otel din da jirgin sama ne na da damar dibar fasinjoji 5,000.
Martanin jama'a
Masu amfani da yanar gizo sun tofa albarkacin bakinsu:
@nalomal0 ya ce: "Um ina shakkar idan injinan zasu iya daukar tsawon shekaru suna aiki. Shi ba kamar mota bane da zaka iya tsayarwa... Idan aka samu matsala ku sa ran kowa zai mutu."
@zemer188 ta ce: "Ba zan so zama cikinshi ba, zan ji kamar an garkame ni kamar zan iya zuwa wuraren, amma ba zan iya zuwa wurare marasa ma'ana irin wannan ba."
@wilkad ya ce: "Ba wannan maganar!! Tashi a sararin samaniya a irin wannan wurin barazana ne ga lafiyar ka, baya ga haka waye zai so numfashi yadda yake so amma ya takure a wurin da ba zai samu isashiyar iska ba."
@timberw0lf ya ce: "Za ka more rayuwa kuma za ka yi wasanni har zuwa lokacin da wannan jirgin ya bigeka da faduwar sawu 10 abun dariya."
Asali: Legit.ng