Malaman Addinin Musulunci Ga Gwamnatin Najeriya: Ku Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Tsaro

Malaman Addinin Musulunci Ga Gwamnatin Najeriya: Ku Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Tsaro

  • Kungiyar limamai da malaman addinin musulunci na Jihar Ogun ta bukaci gwamnatin tarayya da mayar da hankali kan tsaro da ilimi
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Dhikrullahi Afe-Babalola da Babban Sakatarenta, Tajudeen Mustapha
  • Malaman da limaman sun kuma shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wurin kawo gyara a makarantun gaba da sakandare tare da cikawa malaman alkawurran da ta dauka musu

Jihar Ogun - Kwamitin limamai da malaman addinin musulunci ta Jihar Ogun ta ce dole gwamnatoci a dukkan matakai su mayar da hankali kan ilimi da gina al'umma don kasar ta cigaba.

Daliban makarantan gwamnati a Najeriya.
Malaman Addinin Musulunci Ga FG: Ku Mayar Da Hankali Kan Ilimi Da Tsaro. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ta kuma bukaci gwamnatoci su nuna cewa da gaske suke yi wurin daukan matakan kare rayuka da dukiyoyin mazauna kasar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kwararru: El-Rufai zai dauki malamai 10,000 aiki bayan ya kori sama da 2,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku cika wa malaman makarantun gaba da sakandare alkawurran da kuka yi musu, Malaman musulunci ga FG

Kungiyar addinin musuluncin ta bukaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali don sauya mummunan halin da ilimin makarantun gaba da sakandare ke ciki ta kuma cika dukkan alkawurran da ta yi ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar malaman ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Dhikrullahi Afe-Babalola da Babban Sakatarenta, Tajudeen Mustapha kan halin da kasa ke ciki.

Malaman addinin musuluncin sun shawarci gwamnatin tarayya ta yi jagoranci wurin gyara ilimin a makarantun gaba da sakandare da dawo da darajar su.

Shugaban ASUU Ya Ƙi Karbar Tallafin N50m Daga Ahmed Isah Don Janye Yajin Aiki

A wani rahoton, wani abu mai kama da dirama ya faru a lokacin da kungiyar malaman jami'o'i na Najeriya, ASUU ta ki karbar kudin da Berekete Family Radio ta bata don janye yakin aiki, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya bayyana ainahin wadanda ke haddasa rikicin addinai a Najeriya

ASUU ta fara yajin aiki ne tun watan Fabrairu kuma kawo yanzu duk wani yunkuri da aka yi na ganin malaman sun koma aji bai yi wu ba.

A safiyar ranar Asabar, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo, Ahmad Isah, da aka fi sani da Ordinary President ya gayyaci shugaban ASUU don yi wa yan Najeriya bayani kan matsalolin da suke fuskanta da dalilin da yasa ba su janye yajin aikin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel