FG: 'Yan Ta'adda ne ke Zagon-Kasa ga Wutar Lantarkin Yankin Arewa Maso Gabas

FG: 'Yan Ta'adda ne ke Zagon-Kasa ga Wutar Lantarkin Yankin Arewa Maso Gabas

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa 'yan ta'adda ne ke zagon -kasa ga wutar lantarkin Najeriya ballantana arewa maso gabas
  • Ministan wutar lantarki ya sanar da yadda aka taba kai kayan aikin kwangilar wutar, amma mabarnata suka sace wanda hakan ya kawo tsaiko ga aikin
  • Aliyu ya sake bayyana yadda FEC ta amince da wasu ayyukan wutar lantarki kuma jami'an tsaro na kokarin ganin sun hana 'yan ta'adda zagon kasa

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce 'yan ta'adda ne ke kawo ci baya a kokarin da ake na samar da tsayayyar wutar lantarki mai dorewa ga 'yan Najeriya, musamman yankin arewa maso gabas.

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ya fadi hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa Villa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC

Wutar Lantarki
FG: 'Yan Ta'adda ne ke Zagon-Kasa ga Wutar Lantarkin Yankin Arewa Maso Gabas. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana yadda FEC ta amince da kwangilolin wuta da ruwa da dama wadanda suka kai kimar N23,047,974,090.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministan ya kafa misali da abun da ke faruwa a arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, inda ya ce bayan an kawo kayayyakin wutar lantarki da barayi suka sace gami da sake maidawa, ana kara barnatawa.

"Amma a halin yanzu, mun maido da 'dan kwangila don a sake saka babbar turansufoma 330 da aka barnata wani lokaci a baya. Saboda samun isasshiyar wutar lantarki a Damaturu da kewaye, daga kananan ofishin Damaturu tare da kai wani daga cikin Maiduguri, wanda aikin zai habaka wutar lantarkin da kananan ofishin lantarkin Damaturu," kamar yadda ya bayyana.

Haka zalika, ministan ya ce ma'aikatansa basu samu damar tattaunawa da wadanda aka barnata musu kayayyakin lantarkinsu ba a jihar Neja, wadanda suka hada da Shiroro don jin matsalarsu saboda matsalar rashin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

Sai dai ya ce jami'an tsaro na hada kai da ma'aikatansa don magance matsalar.

Borno: An Fallasa Dabarju, Mai Tatsar Wutar Fitillun Kan Titi Yana Kaiwa Gidan Kankararsa

A wani labari na daban, mazauna yankin GRA Maiduguri a ranar Talata sun fallasa wani mutum da ake kira da Dabarju kan satar wutar lantarki daga janareton gwamnati da ake amfani da shi wurin bai wa fitillun kan tituna haske.

Dabarju dai ya mallaki gidan kankara kuma ana zarginsa da tatsar wuta daga janareton gwamnatin.

Sakataren GIS na jihar Borno, Adam Bababe ya jagoranci tawaga wacce ta rushe gini ba bisa ka'ida ba da Dabarju yayi. Tawagar ta kara da kwashe kusan firji 20 da ake amfani da su a gidan kankarar inda tace an dade ana wannan aika-aikar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel