Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9
- Hon. Sergius Ose Ogun ya gabatar da kudiri a zauren majalisa a kan badakalar tallafin man fetur
- ‘Dan majalisar yana zargin an wawuri abin da ya haura Naira tiriliyan 2 tsakanin 2017 zuwa 2021
- Bayan jin jawabin Hon. Ogun, dole Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bukaci a kafa kwamitin bincike
Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman da zai yi bincike a kan sha’anin tallafin man fetur a mulkin Muhammadu Buhari.
Daily Trust ta ce wannan kwamiti zai yi binciken abin da ya faru daga shekarar 2017 zuwa 2021. Sai nan gaba za a samu labarin su wanene za su yi aikin.
‘Yan majalisar kasar sun dauki wannan mataki ne bayan shawarar da Hon. Sergius Ose Ogun ya kawo da yake kokawa a kan yadda NNPC ke aiki a Najeriya.
Sergius Ose Ogun ya ce kamfanin NNPC da wasu masu ruwa da tsaki sun batar da sama da Dala biliyan 10, kuma ba a san inda aka kai wadannan kudi ba.
Ana tuhumar NNPC da sace $7bn
A cewar ‘dan majalisar, a zuwa shekarar 2021, fiye da Dala biliyan bakwai da ya kamata gwamnatin tarayya ta samu daga arzikin mai, sun yi batar dabo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bugu da kari, Hon. Ogun ya ce ana tafka badakala da sunan biyan tallafin man fetur, ana yin mai-mai wajen cire kudi, a haka aka yi awon gaba da fiye da N2tr.
Jaridar ta rahoto ‘dan majalisar yana mai cewa ana tsula kudin da ya kamata a biya kamfanoni na tallafin man fetur, ya ce a irin haka aka dauke makudan kudi.
N70bn Zai bace duk wata - Hon. Ogun
A lissafin Sergius Ose Ogun, NNPC ta na satar Naira biliyan 70 duk wata ko Naira biliyan 840 a shekara. Zuwa yanzu NNPC ba ta maida martani a kan zargin ba.
Tun farko Ogun bai yarda a duk rana ana cin lita miliyan 40 zuwa miliyan 45 na man fetur ba, sannan ya yi Allah-wadai da yadda matatun kasar ba su aiki.
Za a kafa kwamitin bincike - Femi Gbajabiamila
Nan take shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce akwai bukatar a duba abubuwan da ake yi a karkashin tsarin tallafin man fetur a Najeriya.
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya bukaci mataimakinsa da sauran shugabannin majalisa da su kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki zargin badakalar.
Binciken Bukola Saraki ya dauki lokaci
Tun 2019 aka samu labari cewa Lauyoyin EFCC su ka fara binciken Bukola Saraki bisa zargin ya saci kudi daga Baitul malin jihar Kwara a lokacin yana mulki.
Alkalin da ke sauraron shari’a ya yi ritaya, shekaru uku kenan har yau ba a yanke hukunci ba. A zaman da aka nemi ayi a makon nan, an nemi Alkali an rasa.
Asali: Legit.ng